Abu bakwai kan aikin bututu don samar da iskar gas na $2.6bn a Najeriya

Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin shimfida bututun gas din ne ta na'urar bidiyo daga fadarsa

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin shimfida bututun gas din ne ta na'urar bidiyo daga fadarsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani katafaren aikin shimfida bututun iskar gas da zai hada kudanci da arewacin kasar.

Aikin wanda ake sa ran kammalawa cikin shekaru biyu, zai lashe kudi kamar dala biliyan biyu da miliyan dari shida.

Shugaba Buhari dai ya kaddamar da aikin shimfida bututun gas din ne ta na'urar bidiyo daga fadarsa, yayin da sauran jami'ai kuma ke wuraren da za a yi aikin, domin kiyaye ka'idojin ba da tazara na yaki da korona.

Short presentational grey line

Ga dai bayanai kan yadda aikin zai kasance:

  • Aikin zai lashe kudi dala biliyan biyu da miliyan dari shida
  • Kamfanonin China biyu ne za su gudanar da aikin kwangilar shimfida bututun iskas gas
  • Yana da tsawon kilomita 614
  • Ana sa ran za su kammala cikin shekaru biyu
  • Aikin zai fara daga garin Ajaokuta da ke jihar Kogi a tsakiyar Najeriya, zai ratsa ta Abuja babban birnin kasar da jihar Kaduna kana ya dangana da jihar Kano da ke kuryar arewa maso yammacin kasar - abinda zai ba da damar jigilar isakar gas tsakanin kudanci da arewacin kasar ta bututu
  • Wasu cibiyoyin kudi na kasar China biyu ne za su bayar da lamunin kudin aiki - wato Bank of China da kuma Bankin Bada Rance da Inshora na China wato SINOSURE a takaice
  • Shugaba Buhari ya ce yayin da aka kammala aikin, zai taimaka gaya wajen bunkasa masana'antu da samar da ayyukan yi da kuma wutar lantarki a kasar.
Short presentational grey line
Short presentational grey line

Najeriya dai ita ce kasa mafi tattalin arzikin a Afirka, kuma daya daga cikin kasashe mafiya arzikin man fetur a duniya tare da dumbin albarkatun gas, amma masana na cewa galibin albarkatun na gas na kasar ba a cikakken amfani da su yadda ya kamata, ko an bari suna sirracewa a banza.

buhari a taron bututun iskar gas

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Sauran maalarta taron ta bidiyo sun hada da wasu gwamnaoni da manyan 'yan kasuwa

Yayin kadamar da aikin shimfida bututun, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kasar ta dauki darasi daga abinda annobar korona ta haifar, ko ke haifarwa.

Wannan layi ne