Aikin N-Power 2020: Yadda za ku nemi aikin da ke tallafa wa matasan Najeriya

N-Power 2020 registration

Asalin hoton, NPower

Bayanan hoto, N-Power wani shiri ne na kirkirar ayyuka da tallafi karkashin Shirin Bunkasa Al'umma da Kyautata walwalarsu na gwamnatin Najeriya.
    • Marubuci, Fiona Equere
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin
  • Lokacin karatu: Minti 3

Shirin gwamnatin Najeriya na samar wa matasa aikin yi na N-Power, ya ja kunnen 'yan kasar kan cewa neman aikin kyauta ne ba a karbar kudi.

Hakan na zuwa ne a lokacin da suka wallafa wani sakon tiwita cewa wasu mutanen sun fara kokarin yin rijista tun kafin hukumar da ke da alhakin hakan ta bude fara rijistar a eranar Juma'a 26 ga watan Yuni.

Shirin na N-Power ya ce dukkan wadanda suka yi rijistar kafin wannan lokacin to sun yi kuskure don ba za a duba nasun ba.

N-Power wani shiri ne na kirkirar ayyuka da tallafi karkashin Shirin Bunkasa Al'umma da Kyautata walwalarsu na gwamnatin Najeriya.

An samar da shirin ne don taimakon matasan Najeriya.

Rahotanni sun ce gwamnati ta shirya daukar mutum 400,000 da za su ci gajiyar aikin nan.

Ga yadda za ku bi ku yi rijistar Shirin N-Power 2020

A wannan rukuni na C na watan Yunin 2020 masu neman aikin za su yi rijista ne ta intanet a www.npower.fmhds.gov.ng website.

Sannan ba kowa ne zai iya neman aikin ba, sai wadanda shekarunsu ke tsakanin 18 da 35.

Ga abubuwan da kuke bukata a hannun kafin ku nemi aikin:

  • Lambar tantance asusun ajiya na banki (BVN)
  • Karamin hoto da ake kira fasfo na jpeg ko PNG
  • Adireshin i-mail ko lambar wayar wajen aikin
  • Sakamakon digiri ko takardar shaidar kammala yi wa kasa hidima
Yemi Osinbajo

Asalin hoton, @ProfOsinbajo

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar tawagar tattalin arziki
  • Ga abin da ake bukatar ku yi da zarar kun shiga shafin intanet din yin rijistar:
  • Ku sanya bayanin inda za a same ku (adireshin i-mail da lambar waya) a bangaren da aka ware don yin hakan.
  • Bayanan da kuka sanya din zai kai ku cikin i-mail dinku don ku tabbatar da hakan.
  • Da zarar kun tabbatar da adireshin i-mail dinku, sai ku cike wajen da aka tanada don sanya lambobi 11 na tantance asusun ajiya na banki (BVN) sannan ku sanya ranar haihuwa ta hanyar farawa da ranar kwanan wata, sai watan haihuwar sa ikuma shekarar haihuwar taku (dd/mm/yr)
  • Shafin dan bayani a kanku da kuma na tuntubarku: ku sanya sunan kak, sunanku na yanka da kuma sunan mahaifi, kamar yadda yake a bayanin tantance asusun ajiyarku na banki BVN.
  • Shafin bayani kan Ilimi da Shirin: a wannan bangaren za ku sanya matakin iliminku. An bude shirin na N-power ne ga kowa da kowa.
  • Shirin N-Tech da N- health kuwa an bude su ne kawai ga masu shaidar kammala digiri.
  • Shirin N-Power na bangaren Lafiya na masu digiri da HND da OND ne kamar wadanda suka karanci aikin likita da aikin jinya da Ilimin Tsirrai da Unguwarzoma da Ilimin Sanin Hallayyar dan adam da Ilimin halittun da ido ba ya gani wato Microbiology.
  • Kuna bukatar sanya takardar shaidar digirinky a komfuta don aikewa da shi a yayin yin rijistar.
  • Shafin bayani kan aikin da aka taba yi da kuma sauran bayanai: Za ku amsa wasu tambayoyi tare da sanya katin shaida. Ga dai katin shaidar da gwamnati ta yarda ku yi amfani da su a kasa:
  • Fasfo din tafiye-tafiye
  • Katin shaidar zama dan kasa da hukumar NIMC ta bayar
  • Ingantaccen lasisin tuka mota
  • Katin zabe na dindindin
  • Shafin da za ku sake duba bayanan da kyau sannan ku aike
  • Ku duba bayanan da kuka cike duka sannan ku aike
  • Bayan kun aike za ku samu wata lamba ta musamman, sai ku dauke ta ku adana ta da kyau.
Wannan layi ne

Mutanen da suka cancanci shiga shirin

Hukumomi sun ce shirin zai dauki mutum 400,000 da za su yi aiki a bangarori da dama da suka hada da Noma da lafiya da koyarwa da gine-gine da fasaha

A shekarar 2016 ne geamnati ta samar da shirin kuma zuwa yanzu an tallafa wa mutum 500,000.