Cutar Sikila: Abubuwa bakwai da ba ku sani ba game da cutar

Asalin hoton, ARAFA SALIM SAID
Cutar sikila ko amosanin jini na ɗaya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS.
Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al'umma baki daya.
An ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar yaƙi da cutar amosanin jini wato sikila a duniya. Rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin faɗakar da al'umma kan wannan cutar a duniya.
Kan haka ne BBC ta yi nazari kan wasu abubuwa bakwai dangane da cutar:
1. Najeriya ta fi yawan masu cutar a duniya
Bincike ya nuna cewa duk shekara ana haihuwar jarirai 300,000 a duniya kuma rabi daga wannan yawan a Najeriya ake haihuwar su. Daga cikin 150,000 na Najeriya ɗin, 100,000 ne ke mutuwa duk shekara.
Alƙaluma sun nuna cewa mafi yawan masu cutar suna arewacin ƙasar ne. Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewar rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka rawa sosai wajen haifar yara masu ɗauke da cutar sikila a ƙasar.
2. Shan magunguna har abada
Masu fama da cutar sikila suna fara shan wasu magunguna tun daga lokacin da aka gano suna ɗauke da cutar har zuwa ƙarshen rayuwarsu, kamar yadda Dr Bashir Isa Waziri, wani likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano ya shaida wa BBC.
''Daga cikin magungunan akwai 'Folic Acid' wanda yake ƙara musu jini, saboda ƙwayoyin jininsu na saurin ƙarewa. Akwai kuma 'Paludrine' magani ne da ke kare su daga kamuwa da cutar maleriya don tana wahalar da su sosai idan suka kamu.
Sai maganin 'Peniciillin V' shi kuma aikinsa shi ne kare su daga cututtuka masu alaƙa da numfashi. Sai 'Hydroxyurea' wanda yake taimaka wa ƙwayoyin jinin siffarsu ta zama mai kyau, yake kuma taimaka musu wajen rage tashin ciwon. Amma yawanci shi sai wanda ciwon ke masa tsanani,'' in ji likitan
3. Yawaita shan ruwa
Yawan shan ruwa abu ne mai matuƙar muhimmanci ga masu cutar sikila saboda rashin ruwa yana tayar musu da ciwon kwankwaso da na gabobi.
Sannan shan ruwan na sa jini ya dinga gudu yadda ya kamata kuma ƙwayoyin jini su dinga wucewa cikin jiyoyi, wanda haka ke hana ciwon yawan tashi.
4. Zafin ciwon ya fi na naƙuda
Tsananin zafin ciwon kwankwaso da masu cutar kan yi fama da shi lokaci zuwa lokaci yana matuƙar uzzura musu. Ƙwararru a harkar lafiya sun ce zafinsa ya fi na naƙuda.
Dr Bashir Waziri ya ce: "Suna jin ciwon ƙashi kamar ana kwankwatsa shi, jini ba ya isa wasu wuraren don haka idan suka taru a waje ɗaya sai su saka ciwo.''
5. Shafar lafiya jima'i
Likitan ya kuma ce ciwon bai bar masu shi ta ɓangaren shafar lafiyar jima'insu ba.
''Ga maza dai, yawanci gabansu yakan miƙe ya ƙi sauka, ƙwayoyin jini masu kamar lauje na maƙalewa a gabansu sai jinin ya ƙi fita ya taru a wajen, sai al'aurarsu ta miƙe ta ƙi sauka.
''A wasu lokutan har sai an yi ƴar ƙaramar tiyata, wasu kuma da an sanya ƙanƙara sai ta taimaka wajen kwantar da gaban,'' in ji Dr Bashir.
6. Kuka da ihu ba babba ba yaro
Tsananin zafin da ciwon ke zuwa da shi kan sa masu fama da shi su dinga gurzar kuka tare da gunji da gurnani. A irin wannan yanayi ba babba ba yaro, za a ga sun fita hayyancinsu.
Wata mai fama da wannan lalura da ba ta so a faɗi sunanta ta ce: ''Ba zan iya kwatanta yadda ciwon yake ba, illa iyaka zan ce nakan ji kamar an kwankwatsa min kashina da guduma. Shi ya sa duk dauriyar mutum sai an ji sautin kukansa.''
7. Karaya ba tare da jin ciwo ba
Dr Bashir ya ce daga cikin wasu abubuwan mamaki dangane da wannan ciwo shi ne yadda a wasu lokutan sai ƙashin wata gaɓa ta jikin masu ciwon ya karye ɓal.
''Ba komai ke jawo hakan ba sai tsabar zafin ciwon da ke taso musu,'' in ji shi.












