ISWAP ta nemi Najeriya ta biya fansar sama da N190m kan ma'aikatan agaji

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bidiyon da kungiyar ta saki ya nuna mutanen da take tsare da su na neman gwamnatin Najeriya ta kai musu dauki

Mayakan kungiyar Boko Haram ɓangaren Albarnawi wato ISWAP sun bukaci a ba su dala dubu ɗari biyar kwatankwacin N190m kafin sakin wasu ma'aikatan agaji huɗu da wani jami'in tsaro da suka kama.

Cikin wani hoton bidiyo da ƙungiyar ta fitar a farkon makon nan, an nuna waɗanda aka kama na rokon gwamnatin Najeriya ta kuɓutar da su.

Mutanen sun hadar da wani jami'in ƙungiyar agaji ta Action Against Hunger da na ƙungiyar Reach International da kuma na International Rescue Commitee da wani jami'in hukumar ba da agaji ta SEMA hadi da wani jami'in tsaro mai zaman kansa.

Wata sanarwa da kungiyar agaji ta Action Against Hunger ta fitar na cewa an kama mutanen ne tun a watan jiya,.

Ko da a shekarar 2019, sai da ƙungiyar ISWAP ta kashe wasu ma'aikatan jin ƙai guda shida na ƙungiyar Action Against Hunger da ta yi garkuwa da su.

Shin gwamnatin Najeriya zata biya diyyar ?

AFP

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, ISWAP ta saba kashe mutanen da take garkuwa dasu idan aka gaza biyan diyya

Wani mai bincike kan ayyukan ƙungiyoyin ta-da-ƙayar-baya a Afirka, Barista Bulama Bukarti, ya faɗa wa BBC cewa ya danganta da wanda aka kama, akwai wadanda ake biya akwai kuma waɗanda ba a biya.

''Daga mutanen da aka kama, ba lallai ne gwamnati ta fuskanci matsin lamba ba, don haka ba lallai ne a biya kudin ba''.

Ya bayyana cewa lamarin abin takaici ne, domin biyan kudin zai iya bai wa mayakan ƙarin ƙwarin gwiwa don sake kama wasu mutanen da za su ci gaba da neman kuɗin fansa a nan gaba.

Sai dai ya ce ƙin biyan kuɗn kuma zai iya janyo halaka ma'aikatan agajin kamar yadda hakan ta sha faruwa a baya.

To sai dai ɗaya daga cikin kungiyoyin da aka kama jami'an su wato Action Against Hunger, ta ce tana ƙoƙarin ganin ta ceto nata jami'in.

Me jami'an tsaro ke cewa ?

@NigerianArmy

Asalin hoton, @NigerianArmy

Bayanan hoto, Shugaban rundunar sojin Najeriya Yusuf Tukur Burutai

BBC ta yi kokarin jin ta bakin shalkwatar tsaron Najeriya a kan batun, sai dai har zuwa yanzu ba su amsa kiran wayar da muka yi musu ba.

Rundunar sojin Najeriya dai ta sha cewa tana yin iya bakin kokarinta don shawo kan matsalolin tsaro a jihohin arewa maso gabas da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita, amma har yanzu Boko Haram, na da tasiri.

An shafe tsawon fiye da shekara 10 hukumomi a Najeriya suna yaƙi da ƙungiyar Boko Haram - wadda ta yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da lalata dukiya ta miliyoyin naira.

Rikicin wanda aka faro a jihar Borno da ke arewa maso gabas ya fantsama zuwa makwabtan ƙasashe kamar su Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

Gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da rundunar sojin kasar sun sha yin iƙirarin karya lagon Boko Haram, sai dai har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da zamewa ƙasashen yankin Tafkin Chadi barazana.