Coronavirus a duniya: Shin biranen za su fi kyawu bayan wucewar annobar?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Valeria Perasso
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliya kan Harkokin Walwala, BBC World Service
"Zaman birni da kuma kamuwa da cutar tamkar hanta da jini ne."
Farfesa Beatriz Colomina ta Jami'ar Princeton ta kwashe ɗaukacin rayuwarta ta koyarwa tana nazari kan yadda manyan annobobi da cututtuka suke sauya biranen da muke rayuwa a cikinsu.
Da take tsokaci kan tarin-fuka, ɗaya daga cikin manyan cututtukan da suka addabi duniya, Farfesar ta ce: "Ilimin zana gidaje ya sauya sakamakon aukuwar annobar tarin-fuka."
Wannan ba wani abu ne mai ban mamaki ba. Rayuwar birane tana cikin abubuwan da annobar korona ta fi shafa, kamar yadda hakan ya faru a lokutan wasu annobobi da suka gabata.
Mun ga yadda yankunan da mutane suka fi yin cincirindo suka zama tamkar cibiyoyin yaduwar cututtuka, sannan wuraren da a baya mutane suka fi zirga-zirga sun koma kamar kufayi, kana tutunan da ko da yaushe suke cike da jama'a, suka zama tamkar maƙabarta.
A yayin da rahotanni suka nuna cewa mutum fiye da miliyan takwas sun kamu da cutar korona a faɗin duniya, cutar ta tilasta wa kashi ɗaya cikin uku na al'ummar duniya zaman kulle, kuma ta sauya rayuwar mutanen da aka bari su rika fita saboda muhimmancin ayyukansu.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
"Kun san darasin da aka soma koya? Mun soma sake tunani kan yadda rayuwa a birni take, bayan mun fahimci cewa kowa yana iya kamuwa da cutar, daga lebura zuwa shugaban kasa," a cewar masaniya a kan tarihin birane Katrina Johnston-Zimmerman.
Masu tsara sun cika da murna; da dama daga cikinsu suna kallon annobar korona a matsayin wata dama ta gina birane masu inganci.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa fiye da kaso biyu cikin uku na al'ummar duniya za ta zauna a birni daga yanzu zuwa 2050, wato kaso 56 kan yadda ake a yanzu.
Tuni wasu birane suka kaddamar da wasu shirye-shirye na birni don magance cutar korona - sai dai abin tambayar shi ne: shin wannan sauyi zai iya zama na dindindin, kuma zai amfani al'umma?
Zaman gida da daɗi
Annobobin da aka yi a baya sun kawo sauyi daban-daban game da rayuwar birane.
Annobar amai-da-gudawa da aka yi a shekarun 1830 a London ta sa an samu sauyi kan magudanan ruwa, yayin da annobar tashin-fuka da ta faru a karni na na ashirin ta taimaka wurin samun sabbin fasalin birane wadanda muke gani yanzu - inda aka fafaren katangu, da manyan tagogi, da harsasan gini da aka dora dogayen gine-gine a kansu nesa da ƙasa yadda cututtuka ba za su iya yaɗuwa ba.

Asalin hoton, Peter Thompson/Heritage Images/Getty Images
Ɓarkewar da annobar cutar numfashi mai suna Severe Acute Respiratory Syndrome (SARS) ta yi a shekarar 2003 ya tilasta wa Singapore inganta tsarin kiwon lafiyarta, abin da ya sa kenan ta yi hanzarin tunkarar annobar korona.
A wannan karon, masana sun ce annobar Covid-19 ta sa dole a sake nazari kan tsarin gina gidaje.
"An ba mu shawarar zama a gidajenmu, cewa su ne wurin da za mu tsira daga kamuwa da cutar. An ce fita waje zai iya yin sanadi mu kamu da cutar," a cewar masaniya tarihin fasalin gine-gine Farfesa Colomina.
Miliyoyin mutane ne suka koma gudanar da rayuwa a cikin gidajensu, kuma a mataki na ba safai ba, gidajen sun zama wuraren ayyukanmu.
Farfesa Colomina ta ce hakan bai taba faruwa ba tun bayan Industrial Revolution wanda ya bambanta rayuwar gida da ta wurin aiki.

Asalin hoton, Himanshu Bhatt/NurPhoto
A yayin da ake ci gaba da zama cikin dokar kulla sannan mutane suna yin ayyuka daga gidajensu, yanzu mutanen da ke fita su yi tafiya a kan ababen hawa sun yi matukar raguwa kuma ana gudanar da rayuwa tsakanin gida-da-gida.
Masu tsara birane na kallon hakan a matsayi wani abu da zai ci gaba da faruwa - suna kiransa da suna 'sabuwar rayuwa'.
"Idan za ka iya gina gida ta hanyar amfani da kayan aiki masu ƙarko da kudi ƙalilan, hakan shi ne mafi kyawu," in ji Ms Johnston-Zimmerman a hirarta da BBC.
"Mutane da dama sun sake gano irin fasahar da suke da ita. Maganar ita ce, idan aka tilasta maka sauya tunani kan wani abu, daga karshe za ka ga ka yi shi cikin inganci."
Daya daga cikin fasalin da suka sauya harkar gine-gine shi ne shirin "15-minute city", wanda shugabar birnin Paris Mayor Anne Hidalgo take tattalawa da niyyar rage cunkoson ababen hawa da kuma hana abubuwan hawa masu fitar da hayaki da yawa hawa kan fituna lokacin annobar korona.

Asalin hoton, Getty Images
Hidalgo tana so a sauya fasalin birnin Paris yadda mazauna birnin za su iya samun dukkan kayan bukatunsu a tazarar minti 15 daga gidajensu.
"Daga zuwa asibiti, ko kai 'ya'yanka makaranta, ko kuma zuwa lambu don shakatawa... dukkan wadannan. [Sannan] mutum ya samu aiki a wurin da ba shi da nisa daga gidansa," a cewar Jean Louis Missika, mataimakin Hidalgo wanda kuma yake cikin wadanda suka kawo sabon tsarin.
Samun komai a wuri guda zai taimaka wurin rage radadin zirga-zirgar ababen hawa, sannan ya rage cunkoson mutane a manyan birane.
Sai dai hakan ba zai tabbata ba, sai an "kirkiri ofisoshi a yankuna da ake gina gidaje, da kuma wuraren da ake gudanar da kasuwanci," a cewar Mr Missika a hirarsa da shirin The Enquiry na BBC.

Asalin hoton, Corbis/Getty
Masu adawa sun ce wannan shiri zai gagari yin aiki a Paris, birnin da ya fi yawan al'umma a kasashen Turai, har ma da sauran birane da ke bunkasa a kasashe da ke tasowa.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Kotchakorn Vora-akhom

Asalin hoton, Barcroft Media/Getty

Asalin hoton, M. Valdés

Asalin hoton, RAUL ARBOLEDA/ AFP

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Mike Kemp / Getty Images

Asalin hoton, Pallava Bagla / Getty Images











