Evariste Ndayishimiye: An rantsar da sabon shugaban kasar Burundi

Asalin hoton, Getty Images
An rantsar da sabon shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye ranar Alhamis - wata biyu gabanin yadda aka tsara.
Kamfanin dillanacin labaran AFP ya ruwaito cewa an gaya wa mahalarta bikin shan rantsuwar su je da wurwuri domin a samu damar daukar matakan hana kamuwa da cutar korona irin su wanke hannu da gwajin zafin jiki.
An matso da rantsar da shi gaba ne saboda mutuwar farat- ɗaya da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya yi makon jiya.
Mr Ndayishimiye tsohon shugaban 'yan tawaye ne, kamar Mr Nkurunziza.
Mr Nkurunziza ne ya goyi bayansa a zaben shugaban kasa da aka yi a watan Mayu, wanda aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, ko da yake 'yan hamayya sun ce an tafka magudin zabe.
Mr Nkurunziza ya mutu ranar 8 ga watan Yuni yana da shekara 55 bayan ya yi fama da bugun zuciya, a cewasr gwamnatin kasar. Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce ya yi fama da cutar korona.
A watan Agusta aka tsara Shugaba Nkurunziza zai mika mulki ga Mr Ndayishimiye bayan ya kashe shekara 15 yana shugabancin kasar.
Kundin tsarin mulkin Burundi ya bukaci a rantsar da shugaban majalisar dokoki idan shugaban kasa ya mutu yana kan mulki, don haka a bisa doka Pascal Nyabenda ya kamata ya zama shugaban kasar.
Sai dai bayan hukuncin da kotun tsarin mulki Burundi ta yi, an matso da bikin rantsar da Mr Ndayishimiye a Gitega, babban birnin kasar.

Taƙaitaccen tarihin Evariste Ndayishimiye
Sharhi daga Cyuzuzo Samba, BBC News, Nairobi
Sabon shugaban na Burundi mai shekara 52 ana masa kallon mutum ne kamili mai kuma addini
Sai dai yana cikin manyan hafsoshin soji masu ƙarfin faɗa aji tun 2005 lokacin da amininsa kuma abokinsa na tawaye Pierre Nkurunziza ya kwaci mulki.
Manjo Janar Eariste Ndayishimiye, wanda ake kira Neva an haife shi ne a 1968 a lardin Gitega, cibiyar siyasa a Burundi.
Masanin shari'a ne a Jami'ar Burundi, yana karatun shari'a ne a lokacin da yaƙin basa ya ɓarke a 1993 bayan kisan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na farko Melchior Ndadaye.

Kamar magabacinsa Pierre Nkurunziza, a 1995 Mr Ndayishimiyeya tsallake rijiya daga kisan da aka yi wa daliban Hutu Jami'a a Buzumbura, daga nan ne ya tsere daga ƙasar ya bi ƴan tawayen da aka ƙirkira domin yaƙar gwamnatin Tutsi a lokacin .
Mista Ndayishimiye ya goyi baya tare da yin aiki tare da Pierre Nkurunziza a yayin tattaunawar zaman lafiya ta Arusha tsakanin Gwamnati da 'yan tawayen FDD.
yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a 2003 ta kai ga raba madafan iko tsakanin 'yan tawaye da gwamnati, inda Mr Ndayishimiye ya zama mataimaki ga babban hassan sojin Burundi a lokacin, abokinsa kuma Nkurunzizqa ya zama ministan cikin gida.
A 2006 aka ba shi mukamin ministan cikin gida kafin ya zama mai ba shugaba Nkurunziza shawara kan sha'anin soja. Bayan shekaru 10 kuma aka nada shi babban sakataren jam'iyya mai mulki ta FDD har zuwa watan Janairun 2020 da marigayi Nkurunziza ya zabe shi matsayin wanda zai gaje shi.
Mr Ndayishimiye, yana da ƴaƴa shida kuma mabiyi ɗariƙar Katolika ne.
Sai dai ya zama shugaban kasar da aka mayar saniyar ware ta fuskar diflomasiya da bata da wata kyakkywar alaka da masu bayar da tallafi saboda munanan ayyukan keta hakkin dan adam da ake zargin wanda ya gada da aikatawa.












