Iran ta taƙaita tsarin iyali don ƙara yawan al'ummarta

Iran ta taƙita ayyukan bayar da kulawa ga tsarin iyali a asibitocin gwamnatin ƙasar domin bunƙsa yawan al'ummar ƙasar.

Daga yanzu an daina yi wa maza tiyatar daina haihuwa a asibitocin gwamnati sannan kuma sai matan da lafiyarsu ke cikin hatsari ne kaɗai za a ba su maganin hana ɗaukar ciki.

Sai dai za a ci gaba da yin su a asibitoci masu zaman kansu.

Gwamnati ta damu da ƙrancin haihuwa da kuma yawan shekarun al'umma.

Ƙaruwar adadin al'ummar ƙasar na shekara ya ragu kda ashi daya cikin 100 kuma, idan ba a ɗuki mataki ba, Iran za ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi tsufa duniya nan da shekara 30, a cewar ma'aikatar lafiyar ƙasar.

Shekara biyu da suka gabata ne aka ruwaito al'ummar ƙasar sun ƙaru da kashi 1.4%. Iraƙi maƙociyarta, na da kashi 2.3%, Saudiyya na da 1.8%, in ji bayanan Bankin Duniya.

Yawan auratayya da haihuwa na ƙara yin ƙasa a Iran, a cewar kamfanin dillancin labaran ƙasar mai suna Irna, mafi yawa saboda matsin tattalin arziki.

A watan da ya gabata, Mataimakin Ministan Lafiya Seyed Hamed Barakati ya bayar da rahoton cewa auratayya ta ragu kashi 40% a cikin shekara 10.

"Da irin wannan adadin, za mu zama ɗaya daga cikin tsofaffin ƙasashe a duniya cikin shekara 30," in ji shi.

Iran fuskanci ƙaruwar yawan al'umma bayan juyin juya hali na shekarar 1979 amma sai ta ƙddamar da shirin taƙaita haihuwa.

Shugaban addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei ya sha yin kira ga 'yan ƙasar da su hayayyafa, yana mai cewa yana so mutum miliyan 80 na ƙasar a yanzu su zama miliyan 150.