Iran: Sojojin Iran 19 sun mutu a Tekun Oman yayin atasayen soji

Sojojin ruwan Iran 19 sun mutu sannan an jikkata wasu 15 a wani hari da ya rutsa da jiragen sojojin ruwan ƙasar a Tekun Oman, kamar yadda rundunar sojan ruwan Iran din ta bayyana.

Wata kafar yaɗa labarai a Iran ta ruwaito cewa jirgin Jamaran ya hari jirgin Konarak ne - baki dayansu mallakar Iran - da wani makami mai linzami na gwaji a ranar Lahadi.

A cewar rahoton, jirgin Konarak ya sha kai wa jirage hari a kan tekun, yayin da shi ma aka hare shi.

Rundunar sojan ta ce an yi zabarin jirgin daga ruwa sannan kuma an fara gudanar da bincike.

Lamarin ya faru ne kusa da mashigar ruwan Hormuz, wata hanya mai matuƙar mahimmanci da ake yin safarar kashi 1 cikin 5 na man fetur ɗin duniya.

"A yammacin Lahadi... yayin wani atasayen soja da jiragen ruwa ke yi a ruwan Jask da Chabahar, hatsari ya faru da ya rutsa da jirgin kai ɗauki na Konarak, abin da ya jawo shahadar wasu dakarun sojojin ruwa," kamar yadda rundunar sojan ta bayyana ranar Litinin.

Sanarwar ta ƙara da cerwa an kai jirgin tasha "domin duba lafiyarsa", sai dai ba ta yi ƙarin bayani kan yadda lamarin ya faru ba.