Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Giya ta kashe 'yan Iran 600 da suka sha ta a matsayin magani
Wani jami'i a Ma'aikatar Shari'ar kasar Iran ya ce daruruwan 'yan kasar ne suka mutu sakamakon kwankwadar barasa da ya wuce kima tun bayan barkewar Coronavirus a kasar.
Iran ta kasance daya daga cikin kasashen da annobar coronavirus ta fi kamari da samun gindin zama bayan China.
Alkaluman da hukumomi suka fitar sun nuna cewa kusan mutum 4000 cutar ta halaka… baya ga wasu sama da dubu 62 kuma da ta kama.
Annobar ta haddasa tsoro da fargaba da zaman a zullumi da rashin tabbas a kasar kamar sauran sassan duniya.
A kan hakan ne a fafutukar neman mafita, da a kan ce wanda ruwa ya ci idan aka mika masa takobi ma kamawa zai yi; hakan ya sa aka yi ta yada jita-jita da labaran karya kan hanyoyin kariya da kuma maganin cutar, labaran da aka yi ta yadawa ta shafukan intanet a kasar ta Iran kamar a wasu kasashen.
Duk da cewa an haramta amfani da giya a Iran, wasu sun rika yada rahotannin cewa ai giya tana maganin cutar ta Corona, wannan ya sa wasu mutanen suka karkata ga amfani da wasu nau'uka na ruwan giya mai karfi da aka fi amfani da su a masana'antu saboda karfinsu.
To a yanzu dai sakamakon yadda jama'a suka dimauce har ta kai wasu na amafani da irin wadannan nau'uka na giya domin samun waraka ko kariya daga cutar ta Covid-19, kakakin Ma'aikatar Sharia ta Iran din ya ce bisa ga dukkan alamu hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, wato an gudu ba a tsira ba.
Ya ce a bisa alkaluman da suka tantance akwai mutum 600 da suka mutu a sakamakon amfani da ruwan giyar don samun waraka ko kariya daga cutar, wasu kuma 3,000 giyar ta sa su jinya, tun bayan barkewar annobar a kasar ta Iran.
Abin da ya zamar wa wadanda suka karkata ga amfani da giyar a matsayin maganin cutar ta coronavirus; tamkar gudun harbabbiyar barewa.