Covid-19: BBC Africa ta ƙaddamar da shirin yaƙi da labaran ƙarya

BBC Hausa

Sashen da ke watsa labarai ga kasashen Afirka na BBC, BBC Africa, ya kaddamar da wani shiri na yaki da labaran karya game da cutar korona.

BBC News Africa ta kaddamar da wani dakin karatu na shafin intanet wanda mutane za su iya dubawa domin ganin labaran cutar korona da aka bi diddigi wajen tantance sahihancinsu.

Sashen BBC Africa da BBC Reality Check ne suka gina dakin karatun na intanet wanda ke kunshe da bayanai da ke karyata labarai kamar wanda yake cewa fasahar intanet ta 5G ta taimaka wajen yada cutar korona, ko kuma labarin da ke cewa akwai "wata ilhama" da ke warkar da cutar.

Kazalika an fitar da bayanai cikin hotuna na yadda mutum zai tantance sahihancin labari wadanda za a wallafa a shafukan zumunta.

Shugaban sashen labarai na Afirka a BBC, Solomon Mugera ya ce: "Ganin yadda labaran karya kan annobar korona suke ta waɗari a nahiyar, muna so mu taimakawa masu bibiyarmu wajen raba tsaki da tsakuwa sannan mu ba su sahihan labarai."

A nata bangaren, Shugabar shafukan intanet na BBC Africa Digital Miriam Quansah ta ce: "A yayin da 'yan jarida suke ci gaba da bayar da labaran irin tasirin da COVID-19 take yi a Afirka, wannan shiri zai taka muhimmiyar rawa wajen magance labaran karya ta hanyar bayar da sahihan bayanai."

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus