George Floyd: Yadda Ghana ta girmama bakar fatar da ya mutu a hannun 'yan sandan Amurka

Asalin hoton, Reuters
Cikin jerin wasikun da muke samu daga nahiyar Afrika, 'yar kasar Ghana Elizabeth Ohene ta yi nazari kan George Floyd, wanda kisan da aka yi masa ya janyo zanga-zanga a fadin duniya ta nuna rashin amincewa da nuna wariyar launin fata, an yi zaman nuna alhinin kashe shi a yammacin Afrika inda aka taba yin kasuwancin bayi.
Mun yi jana'iza sosai mu ma a nan Ghana. Kuma idan ana maganar jimami da kide-kiden jana'iza da sanya tufafi da bikin raka mamaci, ina ganin babu wanda ya yi sama da namu.
Bayan na kalli bikin binne George Floyd a talabijin, na fuskanci akwai bukatar tunasar da mafi yawan bakaken fatar Amurka cewa za su iya bin yadda ake yin jana'iza a yammacin Afrika don su kwaikwaya cikin sauki. Ko kuma su shirya zaman nuna bakin ciki da damuwa na mutanen da suke rasawa akai-akai.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin bikin binnewar da ya gudana a Houston ranar Talata, akwai wata shaida cikin sakon ta'aziyyar da shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya aike wa iyalan Floyd.
Ya bayyana cewa za a rubuta sunan George Floyd na har abada a jikin katangar wani zaure na ginin wata cibiyar bakaken fata mazauna Turai da ke Accra babban birnin kasar ta Ghana.
Kuma an yi hakan lokacin bikin binne shi, wanda hukumomin yawon bude ido na Ghana suka shirya a makon jiya, a wani bangare na tunawa da George Floyd, wanda aka kashe akan titi a Minnesota bayan wani dan sanda ya danne wuyansa na tsawon minti 9.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A bara Ghana ta yi bikin juyayin tunawa da cikin bayi da aka yi shekaru 400 da suka gabata.
Shugaba Akufo-Addo ya bayyana shekarar 2019 a matsayin shekarar dawowa gida, tare da tura sakon gayyata ga 'yan Afrika da ke zaune a kasashen waje, musamman jikokin bayin, da su zo Ghana dan ziyara ko kuma komawa can da rayuwa.
Mafi yawan gine-gine da kuma tsarin da aka yi amfani da su lokacin cinikin bayi suna nan a Ghana, a matsayin wani abin tarihi na takaici da za a rika tuna bakaken mutane da su.
Ana kashe Floyd sai labari ya bazu, da yawan mutane sun mai da rikicin nasu.
Kafin barkewar annobar korona muna ta samun tururuwa bakaken fata 'yan Amurka da ke zuwa ziyara.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu antoni janar na jihohin bakake shida sun je Ghana daga Amurka a watan Maris a matsayin shirin dawowa gida, kuma mun karbe su a matsayin bakin mu na ranar samun 'yancin kai da muke bikin a ranar 6 ga watan Maris.
Ciki har da antoni janar na Minnesota Kieth Ellison, wanda yanzu shi ke gabatar da karar zargin kashe Floyd.
Lokacin da hukumar bude ido ta Ghana ta shirya wannan taron, ta dauke shi da muhimmanci kuma hakan ya bayyana a zahiri.
The haunting music of the dirges on the flutes signalled that Mr Floyd was one of our own and we were sending him off to our forefathers"
Daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da aka yi yayin jana'izar shi ne tufafin da aka sa. Wanda suke kokarin bayyana mutumin da aka kashe da kuma yadda ya mutu.
Launin tufafin da ya fi yawa shi ne ja da baƙi da ke nuna mutumin da aka kashe ya mutu ne lokacin da ke tsaka da rayuwarsa, kuma sanadin mutuwarsa aka yi wanda ba a taba zato ba.
Wani abin jin dadinmu ne a Ghana tufafinmu da ya yi shuhura na Kente a ce an yi amfani da shi a matsayin abin nuna juyayi ga mutuwar George Floyd.
Wasu manyan 'yan majalisar Dimokrat sun russuna kan gwiwarsu domin girmamawa ga Floyd kuma sanye da kente a wuyansu.
Mutanen Ghana na matukar alfahari da wannan tufafi. A wani lokaci da ya shuɗe sai da ya zama ana kiran sunan kente a ko ina ikin kasata. Kuma ya zama tufafin manya da masu arziki.
Ana saƙa shi da launuka iri-iri kuma ko wanne da sunansa.
Tafiyar zamani da kuma shiga aikin saka shi da jami'ar Kwame Nkrumah da ke birnin Kumasi ta yi, sai amfani da shi ya koma hannun matsa.
Sai ya zama tufafin sanya wa a taruka na musamman amma yanzu darajarsa ta kara fitowa.

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da jami'ar Ghana ta fara bayan da digirinta, sai ta ratsa launin kente jikin rigar bikin kammala jami'a da kuma lokacin shiga ga sabbin ɗalibai.
Kwanan nan tufafin zai koma alamar kammala makaranta da kuma wasu bkukuwa masu mahimmanci, a kuma ratsa wasu kalamai a jiki don nuna girmamawa.
Mun yi matukar farinciki da bakaken Amurka suka yi amfani da tufafin don tausayawa ga wani dan uwansu, kuma idan wasu za su yi amfani da shi a matsayin sadaukarwa ba za mu yi korafi ba.
Ina ganin a kusa masu saka za su fara ratsa rubutun Ba Na Iya Numfashi jikin tufafin kente, kuma dole mu sanya shi mu yi murna mu tuna da rayuwar George Floyd.












