George Floyd: Za a rusa rundunar 'yan sandan Minneapolis

Protesters hold a placard that reads "Defund MPD (Minneapolis Police Department)" at a rally in Minneapolis, Minnesota. Photo: 6 June 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu masu zanga-zanga sun dade suna kiraye-kirayen a rusa rundunar 'yan sandan birnin
Lokacin karatu: Minti 2

Daukacin kansilolin majalisar gudanarwa a birnin Minneapolis sun yanke shawarar rusa rundunar 'yan sandan birnin, a daidai lokacin da zanga-zanga ke karuwar a fadin Amurka saboda kisan da 'yan sanda suka yi wa wani bakar fata Ba'amurke mai suna George Floyd.

Tara daga cikin kansiloli 13 na majalisar gudanarwar sun ce za su samar da "wani sabon tsarin da za a mayar da hankali ga tsare lafiyar mutanen birnin" da ake tuhumar jami'an tsaro da nuna bambancin launin fata ta hanyar fifita Amurkawa farar fata.

Tun da farko Magajin Garin Jacon Frey ya ki amincewa da a dauki matakin rusa tsarin aikin 'yan sandan birnin, abin da ya janyo jama'a suka rika yi masa ihu.

An shirya binne gawar Mista Floyd ranar Talata a Houston, birnin da ya zauna gabanin komawarsa Minneapolis.

Zanga-zanga ta barke a biranen Amurka bayan da wani bidiyo ya fito a shafukan intanet, inda aka ga wani dan sanda farar fata ya maƙure Mista Floyd a kasa da gwuiwoyinsa na tsawon minti tara.

Hakan ne ya yi sanadin ajalin George Floyd.

An kori dan sandan mai suna Derek Chauvin daga aiki kuma yana fuskantar tuhumar kisan kai.

Sauran 'yan sanda uku da ke tare da Mista Chauvin na fuskantar tuhumar taimakawa ko kin daukar matakin hana abokin aikinsu kashe George Floyd

Kansilolin tara sun karanta wata takarda a gaban daruruwan mazauna birnin a rana ta 13 ta zanga-zangar.

Shugabar majalisar gudanarwar birnin Minneapolis Lisa Bender ce ta jagoranci kansilolin a ganawar da suka yi da masu zanga-zangar:

Ta ce: "Yanzun nan mu kansiloli tara na majalisar birnin Minneapolis mun sanar da kudurinmu na rusa rundunar 'yan sandan Minneapolis, domin gina sabon tsarin samar da tsaro ga al'umomin birnin nan tare da gudunmuwar jama'ar birnin nan."

Kansila Alondra Cano ta aika da wani sakon Twitter jim kadan bayan majalisar birnin ta yanke hukuncin rusa rundunar 'yan sandan:

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A cikin sakon, kansilar ta ce "duka kokarinmu na kawo sauyi sannu a hankali ya gaza. Wannan haka yake ko shakka babu."

Presentational white space

Mis Bender ta ce za a tattauna kan yadda sabon tsarin aikin 'yan sanda zai kasance a kwani masu zuwa, kuma ta ce majalisar za ta yi amfani da kudaden da aka ware wa rundunar 'yan sandan birni ga ayyukan raya unguwannin birnin.

Wannan matakin da mahukuntan birnin Minneapolis suka dauka zai ja hankulan Amurkawa, kuma yana iya kawo wani gagarumin sauyi ga yadda ake gudanar da aikin 'yan sanda a fadin kasar.