Coronavirus a Najeriya: Sabbin ƙa'idojin da filaye jiragen sama suka gindaya

- Marubuci, Daga Fiona Equere
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin
- Lokacin karatu: Minti 1
Bayan sama da watanni biyu da gwamnatin Najeriya ta rufe duka filayen jirgin ƙasar sakamakon cutar korona, a halin yanzu za a ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin jihohi daga 21 ga watan Yuni.
Filayen jirgin sama biyar ne kawai ƙasar ta bai wa damar fara aiki.
Filayen jirgin saman sun haɗa da: Filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da na Murtala Muhammad da ke Legas, sai kuma na Sam Mbakwe da ke Owerri, da kuma na Omagwa da ke Fatakwal, sai kuma na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Sai dai har yanzu ƙasar ba ta buɗe wa jiragen ƙasashen ketare hanya ba domin ci gaba da zirga-zirga ba.

Asalin hoton, FAAN
Ga wasu daga cikin ƙa'idojin da fasinjoji za su bi idan an buɗe filayen jiragen sama
- Dole ne fasinjoji su saka takunkumin rufe fuska kafin a bar su su shiga filin jirgi
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
- Za a rinƙa gwajin zafin jikin fasinjoji
- Hukumomin filayen jirgi za su zana layi a ƙasa da zai nuna wa fasinjoji inda za su tsaya yayin da suke bin layi.
- Za a saka wata maraba ta gilas tsakanin fasinjoji da kuma ma'aikatan jirgi yayin da suke bin layin yankar tikiti domin bayar da tazara.
- Za a saka alama a wuraren zama domin bayar da tazara yayin da fasinjoji ke jiran jirgi.
- Ma'aikatan filin jirgin za su rinƙa nuna wa fasinjoji yadda ya kamata a gudanar da lamura domin gudun karya doka.
- A daidai lokacin da za a shiga jirgi, dole ne kamfanin jirgin saman da za a shiga ya bayar da sinadarin wanke hannu kafin shiga jirgi.







