Faransa ta ce ta kashe jagoran al-Qaeda a arewacin Afirka

Faransa ta ce ta kashe jagoran ƙungiyar al-Qaeda na arewacin Afirka, Abdelmalek Droukdel, a wani samame cikin ƙasar Mali.

Ministar tsaron ƙasar Florence Parly ta ce an kashe Droukdel tare da wasu na hannun damansa ranar Laraba a arewacin ƙasar.

Ta kuma ce dakarun Faransa sun kama wani babban kwamandan ƙungiyar IS yayin wani aikin soji cikin watan Mayu a Mali.

A cewarta samamen na hatsabibanci sun yi mummunar illa ga ƙungiyoyin 'yan ta'addan.

"Dakarunmu, da haɗin gwiwar abokan ƙawancensu a Sahel, za su ci gaba da farautar su ba ji ba gani," in ji ministar.

A matsayinsa na shugaban Al-Qaeda a Maghreb wato (AQIM), Droukdel shi ne jagoran duk rassan ƙungiyar a arewacin Afirka kuma yana jagorantar reshen al-Qaeda a yankin Sahel, wato Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM).

Shi kuma kwamandan ƙungiyar IS da aka kama, Mohamed Mrabat, tsohon mayaƙi ne na masu iƙirarin jihadi kuma ya riƙe babban muƙami a reshen ƙungiyar mai suna Islamic State in the Greater Sahara (ISGS), in ji Misis Florence Parly.

Ta ce an kama shi ne ranar 19 ga watan Mayu.

A ranar 7 ga watan Mayu ne ƙungiyar IS ta bayyana cewa mayaƙanata sun gwabza wani ƙazamin faɗa da takwarorinsu na ƙungiyar Al-Qaeda a Mali da Burkina Faso.

Ta kuma zargi mayaƙan ƙungiyar Jamaat Nusrat al-islam wal-muslimin JNIM da kai hare-hare kan tungoginta tare da datse hanyar da take samun man fetur da kuma tsare magoya bayanta.