AfDB ya wanke Adesina daga zargin nuna ɓangaranci

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar gudanarwar bankin ci gaban Afirka, African Development Bank (AfDB), ta ce bata nemi shugaban bankin, Akinwumi Adesina, ya sauka daga mukaminsa ba.
Hukumar ta ce tana yin nazari da gaske kan zarge-zargen da aka yi wa Mr Adesina.
Amurka ta yi watsi da wani bincike da aka yi a kansa game da zarge-zargen nuna ɓangaranci - sai dai bankin ya wanke Mr Adesina daga zarge-zargen.
Niale Kaba, mai magana da yawun bankin, ta ce babu wata matsalar shugabanci ko ta tsarin mulki a AfDB.
Wasu masu kwarmata bayanai ne suka zargi Mr Adesina da nada 'yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa. Sai dai ya musanta zarge-zargen.
Amurka tana da kashi 6.5 na hannun jari a bankin, kuma ita ce ta biyu mafi yawan hannun jari bayan Najeriya.
Denmark, Norway, Sweden da kuma Finland - wadanda su ma suna da hannun jari a bankin - sun aike da sakon da ke goyon bayan gudanar da bincike mai zaman kansa a kan Mr Adesina.







