Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Rayukan mutanen da suka salwanta saboda labaran ƙarya kan korona
- Marubuci, Daga Marianna Spring
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakili na musamman a yaki da labaran karya
- Lokacin karatu: Minti 6
"Muna tunanin gwamnati na amfani da ita su rikita mu," in ji Brain Lee Hitchens, "ko kuma ta hanyar amfani da tsarin intanet na 5G. Amma bamu bi dokokin ba kuma ba za mu nemi taimako a kusa ba."
Brain mai shekara 46, na magana ne ta waya daga gadon asibitinsa a Florida. Matarsa na matukar fama da mummunar rashin lafiya sosai - an mata allurar barci, a sashen masu bukatar kulawa ta musamman an kuma sa mata na'urar taimaka wa nunfashi.
"Yakin da suke yi shi ne da huhunta," ya ce, cikin tattausar murya. An ta yi mata abubuwa daban-daban jikinta ba ya dauka.
Bayan karanta wani rubutu a intanet game da tuggu kan wannan cuta, sun dauka cutar abar wasa ce - ba su dauke ta a bakin komai ba. Amma a farkon watan Mayu, ma'auratan sai suka kamu da cutar korona.
"Yanzu na yarda cewa korona ba karya ba ce," ya ce, lokacin da yake samun matsalar numfashi. "Akwai ta a ko ina kuma tana ci gaba da yaduwa."
Labaran bogi masu hadari
Wata tawagar BBC na bibiyar yadda labaran bogi ke karuwa tsakanin mutane. Mun biciki gwamman matsaloli irin wadannan - a baya ba a ba da labaran wasu ba - mun yi magana da mutanen da abin ya shafa da kuma hukumomin asibiti a kokarin bankaɗo labaran da suka faru.
Matsalar ta bazu ko ina a fadin duniya.
Jita-jitar da ake yadawa ta yi sanadiyyar kisan taron dangi a Indiya da kuma shakar gurbatacciyar iska a Iran.
An ta yi wa injiniyoyin kamfanonin waya barazana da kuma kai musu hari an kuma kona wani turken intanet a Burtaniya da wasu kasashe - duk saboda wancan labarin tuggun da aka yi kan cutar korona.
Sanya wa guba da nufin wanke abubuwan amfani
A karshen watan Maris ne, Wanda da Gary Lenius suka fara jin magana a kan hydroxychloroquine.
Ma'auratan sun gano irin wannan magani cikin wata kwalba a bayan gidansu a yashe.
Hydroxychloroquine watakila zai iya yakar cutar - amma ana ci gaba da bincike. A bayan-bayan nan ne Hukumar Lafiya Ta Duniya ta dakatar da amfani da maganin tana gargadin cewa maganin zai iya kara hadarin mutuwar masu fama da cutar da wurin.
An ta yada jita-jitar tasirin maganin a China a karshen watan Janairu. Kafafafen yada labarai ciki har da ta kasar sun wallafa wani tsohon bincike kan maganin, lokacin da aka gwada shi a matsayin maganin da ke yaki da cutuka.
Akwai wani likita ya yi ikirarin kwarin gwiwa kan sakamakon. Amma daga baya sai aka bayyana shakku kan binciken.
An kuma ambato tsoro da ake fama da shi a matakai daban-daban, daga kafafen yada labarai zuwa manyan mutane kamar su shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro.
Haka kuma ya samu goyon baya daga fadar White House lokacin da aka yi wa 'yan sanda karin bayani - Kuma Shugaba Trump ya wallafa a Tiwita.
"Me za ka rasa? Ya bayyana hakan ne a ranar 3 ga watan Afrilu. "Ka yi amfani amfani da shi." A tsakiyar watan Mayu, ya ci gaba da cewa - shi yana bin abin da ransa yake so ne.
A ko wanne lokaci akan kara samun ce-ce-ku-ce game da maganin a kafafen sada zumunta in ji wata tawaga da ke bibiyar al'amura a intanet.
Akan sha kwayar magani ta wuce iyaka a wasu lokuta kalilan, amma fargabar da annobar korona ta haifar ya kara adadin yadda ake sha.
A Najeriya, asibitocin da ake kwantar da wadanda suka sha maganin sun yi gargadi ga hukumomin lafiya a jihar Legasdta su ja kunnen mutane kan amfani da maganin.
A farkon watan Maris, wani mutum mai shekara 43 dan kasar Vietnam aka kwantar da shi a wani asibiti da ke lura da wadanda suka sha guba da ke Hanoi bayan sha maganin Chloroquine da ya wuce ka'ida.
Ya bugu yana ta layi ya kasa tsayuwa wajen guda. Likitan da ke shugabantar asibitin ya ce mutumin ya auna arziki ya ga likita da wuri - da ya mutu.
Gary Lenius bai taki sa'a ba. Maganin da suka sha shi da wanda ya kai su kasa saboda yana da wani sinadari na daban, shi ya sa ya zamar musu tamkar guba.
Cikin 'yan dakika kadan, dukkan su suka fara jin zafi da jiri. Sun yi ta amai da kuma kokarin yin numfashi. Gary ya mutu amma Wanda na asibiti.
Daga baya Wanda ta yi bayanin yadda ma'auratan suka sha wannan hadin gambiza.
"Trump ya sha nanata yana cikin kyakkyawar kariya," kamar yadda ya ce.
Gubar sinadar Alcohol
A Iran, Hukumomi sun ce daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu saboda jita-jitar cewa sinadarin Alcohol na maganin cutar korona.
Duka mutanen da suka mutu 796 zuwa karshen watan Afrilu in ji Kambiz Soltaninejad, wani jami'i daga wata kungiyar ma'aikatan lafiya, wanda duk wannan ya faru ne sakamakon yada labaran karya a kafafen sada zumunta.
Amma wannan adadin abin takaici ne a kasar da aka haramta shan barasa kamar Iran.
Wani abin takaici mun gano wani yaro dan shekara biyar ya makance bayan iyayensa sun tuttila masa barasa a kokarin yaki da cutar korona.
"Mun sani labaran bogi kan iya janyo asarar rayuwa," in ji Clare Milme, mataimakin mai tace labarai a wata kungiya da ke bibiyar gaskiya tare da tabbatar da ita, akwai alamun mummunan tasirin cutarwa game da wadannan labarai."
'Abokina ya ci sabulu'
Shugaba Trump ya yi ta shaci fadi game da wasu matakan riga-kafin bayan hydroxychloroquine. A karshen watan Afrilu, ya ce hasken wutar da ake amfani da shi wajen kashe kwayoyin cuta a jikin kayan sawa zai iya maganin korona.
"Naga yadda yake waje da kwayar cuta cikin kankanin lokaci, minti daya. Ina ga akwai hanyar da za mu iya amfani da shi mu shiga ciki sai mu wanku?
Daga baya Trump ya ce bayanin da ya wallafa din zolaya ce kawai. Amma da yawan Amurkawa ba su kalli abin a matsayin zolaya ba, kuma fanni ne da ke kula da wadanda ke shan guba ya ta samun kira domin tambayar shawarwari.
Dakta Maru wani likita ne a asibitin Elmhurt da ke New York, ya ce abokan aikinsa sun warkar da wasu marasa lafiya da wannan hasken kashe cutukan.
Tuggu
Kafafafen sada zumunta sun zama wani filin shirya tuggu, daya daga cikin wanda aka yi kan cutar korona ya janyo asarar sai da dukiyoyi.
A fadin Burtaniya, an lalata sama da turakun wayar salula 70 saboda karyar cewa tsarin intanet na 5g na yada cutar.
Da yawan mutane sun yi ta gangamin wayar da kai game da wannan tsari na 5G, kan cewa yana kara ta'azzara cutar.
Hare-hare
A watan Maris shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebeyesus ya yi gargadin annobar za ta iya haifar da wata sabuwar adawa mai cike da hari.
Yana magana ne kan hare-haren kin jinin mutane a Asiya da China, amma cutar za ta iya munana yanayin da ake ciki a kasashe da dama.
A watan Afrilu an kai wa wasu Musulmai hari su uku a Indiya a wurare daban-daban a Delhi. An musu dukan tsiya bayan an ta yada jita-jitar cewa Musulmai na yada cutar.
An kuma jikkata wasu likitoci a karshen watan Afrilu saboda wannan jita-jita.
'Mun yi rashin rayuka da dama sakamakon labaran bogi'
Da yawan mutane sun mutu saboda labaran karya da suke karantawa a intanet.
Ba wai kashe kansu suke ba amma suna shan magungunan riga-kafin da ba na gaskiya ba, suna rage musu damar yaruwa ba tare da tunanin cutar korona gaskiya ba ce.
A wani yammacin Juma'a a watan Mayu, aka kawo wasu abokai biyu sashen agajin gaggawa sun sha wani abu da ya jefa su cikin matsananciyar rashin lafiya.
A kan idon Dakta Rajeev Ferdando daya ya mutu dayan kuma aka kai shi sashen kulawar gaggawa na wani asibiti a New York aka sa ma shi na'urar taimakawa numfashi.
Daktan ya tambayi mutanen me ya hana su zuwa asibiti da wuri. Sai suka ce sun karanta wani abu a intanet cewa korona karya ce.
"Sai suka gwada wani magani" Dakta Fernando ya ce. "Sun yi tunanin wani abu ne kawai kamar mura."