Buhari ya ce bai soke muƙaman da Abba Kyari ya sanya wa hannu ba

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY
Fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Buhari bai soke mukaman da tsohon shugaban ma'aikansa Malam Abba Kyari ya sanya wa hannu ba.
Wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata, ta musanta cewa Shugaba Buhari ya mika ikonsa na gudanar da mulki ga Abba Kyari.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
"An ja hankalin fadar shugaban kasa kan wasu rahotanni da ke zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya soke wasu ayyuka da nade-nade da tsohon shugaban ma'aikata ya sanya wa hannu.
Bamu yi mamaki ba, saboda rahotannin ba su ambato sahihan majiyoyi ba. Babu kanshin gaskiya a wadannan rahotanni kuma ya kamata 'yan Najeriya su yi watsi da su," a cewar Garba Shehu.
Ya kara da cewa 'yan Najeriya ne suka "sake zaben Shugaba Buhari a watan Fabrairun 2019. Bai sarayar da ikon da 'yan Najeriya suka dora a kansa ba kuma ba zai taba sarayar da shi ga kowa ba."
Masu lura da lamura da dama na ganin idan akwai wani mutum guda da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shi, kuma yake takama da shi a gwamnatinsa, to shi ne marigayi shugaban ma'aikatan fadarsa Malam Abba Kyari.
Hakan ya kara fitowa fili bayan Shugaba Buhari ya umarci ministoci da wasu jami'an gwamnatinsa su tuntubi marigayi Abba Kyari gabanin shigar da duk wata bukata tasu a gare shi.
A baya dai, jami'an gwamnati da dama cikin har da mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, sun zargi tsohon shugaban ma`aikata a fadar, Abba Kyari da yin shisshigi a cikin al`amuran da basu shafe shi ba.
Manjo-Janar Monguno mai ritaya ya ce katsalandan din da Abba Kyari ke yi a aikinsa ya takaita nasarorin da ake samu a kokarin inganta tsaro a Najeriya.
A watan jiya Malam Abba Kyari, ya rasu a Legas inda ya tafi jinya bayan kamuwa da cutar ta korona, yana da shekaru 67 a duniya kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta nuna.










