Me ya sa marigayi Abba Kyari ya yi kaurin suna a Nigeria?

Asalin hoton, Presidency
- Marubuci, Ishaq Khalid
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
A ranar Juma'a 17 ga watan Afirilun 2020 Allah Ya yi wa shugaban ma'aikata a fadar shugaban Najeriya Malam Abba Kyari rasuwa bayan ya yi fama da cutar Korona wadda ta zama annoba a fadin duniya.
Malam Abba Kyari, ya rasu a Legas inda ya tafi jinya bayan kamuwa da cutar ta Korona, yana da shekaru 67 a duniya kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta nuna.
Shi ne babban jami'in gwamnati na farko da cutar Korona ta yi sanadin mutuwarsa a Najeriya.
A rannar 24 ga watan Maris ne aka ba da rahoton cewa marigayin ya kamu da cutar ta Korona. Ana kyautata zaton ya harbu da cutar ne a kasar Jamus yayin wata ziyarar aiki, kafin daga bisani gwaji a Najeriya ya tabbatar yana dauke da ita.
Bayan kimanin makwanni uku yana jinya ya mutu, kana aka dauko gawarsa zuwa Abuja babban birnin kasar inda aka yi masa sutura.
A lokacin rayuwarsa, ana kallon Malam Abba, haifaffen jihar Borno, a matsayin mutum mafi karfin fada-a-ji a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Hasali ma wasu na ganin ya kasance jagoran gwamnatin a kaikaice, saboda yadda suka yi imanin shi ne ke juya akalarta yadda yake so.
Ko shakka babu rawar da ya taka ta janyo masa suka, da bakin jini, yayin da wasu ke yabonsa da sambarka. Mutum ne da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Mutuwarsa ta ja hankulan jama'a matuka a ciki da wajen Najeriya saboda imanin da mutane da dama suka yi cewa rawar da yake takawa a gwamnatin, lokacin da yake raye, na shafar rayuwar miliyoyin jama'ar Najeriya.
Karfin ikon Abba Kyari

Asalin hoton, Buhari Sallau
Masu lura da lamura da dama na ganin idan akwai wani mutum guda da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shi, kuma yake takama da shi a gwamnatinsa, to shi ne marigayi shugaban ma'aikatan fadarsa Malam Abba Kyari.
Masu sharhi na cewa ya fi kowane jami'in gwamnati yawan ganawa da shugaba Buhari.
Watakila wannan asali ya samu, domin shugaba Buhari ya bayyana cewa tun shekaru 42 da suka gabata, wato lokacin marigayin na matashi dan shekara 20 da 'yan-kai, suka hadu kuma suka saba, har zuwa lokacin da mutuwa ta raba su.
Shugaban kasar, a sakonsa na ta'aziyya, ya ce ya yi rashin ''amini kuma mai kishin kasa'' wanda ya yi aiki tukuru a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.
To sai dai masu sharhi da ma wasu talakawan Najeriya na ganin Malam Abba Kyari ya samu iko da karfin fada-a-ji fiye da kima a gwamnatin Muhammadu Buhari inda wasu suka yi zargin cewa shi ke juya akalar gwamnatin a lokacin yana raye.
Wasu na ganin hatta ministoci da sauran masu rike da mukamai, tsohon shugaban ma'aikatan ne ya amince da nadin galibinsu, kuma duk wanda ba ya dasawa da shi, to zai yi wahala ya yi wani tasiri ko samun karbuwa a gwamnatin.
Wannan lamari ya sanya mutane da dama sun kalli Malam Abba a matsayin kadangaren bakin tulu...
Ba mutane na nesa ne kawai suka yi korafi ba. Hatta mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari ta yi korafin cewa wasu mutane 'yan kalilan sun kankane gwamnatin mai gidan nata, suna kuma hana ruwa gudu.
Ko da yake ba ta ambaci sunan wani mutum a bainar jama'a ba, to amma masu lura da lamura da dama na ganin ta bi sahun wasu 'yan Najeriya ne masu korafi kan wasu makusanta shugaban kasar irin su marigayi Abba Kyari.
Wasu na ganin ta yi korafin ne saboda ita ma an hana ta sakat.
Haka nan, a kwanakin baya wasu kafofin watsa labarai a Najeriya sun ambato babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno, na nuna rashin jin dadinsa kan salon Abba Kyari, yana cewa marigayin na yi masa katsalandan cikin aikinsa da ya shafi tsaron kasa.

Asalin hoton, @Bashirahmad
Bayan sake rantsar da shugaba Muhammadu Buhari domin wa'adin mulki na biyu a watan Mayun 2019, shugaban kasar ya tayar da kura lokacin da ya bayyana karara cewa duk wanda ke son ganawa da shi - ko da ministan gwamnatinsa ne ko gwamna - bare kuma bako ko kuma mai ziyara - to dole ya bi ta wajen Abba Kyari.
Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a watan Agustan 2019 yayin rantsar da ministocinsa domin wa'adin mulki na biyu. Wannan lamari ya janyo manyan batutuwa akalla guda biyu.
Wasu na ganin shugaba Buhari ya kara lafta wa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar iko a daidai lokacin da 'yan kasar da dama ke ganin shi ne ma yake hana ruwa gudu a gwamnatin.
Wasu kuma na ganin umarnin shugaban kasar ya kaskantar da ministocinsa duk da cewa bisa tsarin mulki sun fi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa karfin iko ko girman mukami.
To amma jami'an gwamnatin Buhari sun kare matakin da cewa ai da ma Malam Abba Kyari shi ne Sarkin Fada, don haka duk mai son ganin shugbaba sai ya bi ta hannunsa.
Kuma aikinsa a cewarsu shi ne kare muradin shugaba Buhari da kuma tsara jadawalin aiki a fadar shugaban kasar domin kauce wa rudani da tafiyar da lamura rambatsau. Don haka aikin na cikin hurminsa.
Wani mai sharhi kan lamuran siyasa, Dr Abubakar Kari, ya ce wani abu da ya jawo wa Abba Kyari bakin jini kuma ya sa aka kasa fahimtarsa shi ne irin karfin iko da aka ba shi wanda ''ba sabon ba ne a Najeriya''.
Dr Kari ya ce ba a taba yin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da aka bai wa karfin iko kamar marigayin ba.

Salon tafiyar hawainiya
Lokacin da jama'ar Najeriya daga kusan duk sassan kasar suka jajirce suka zabi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya karkashin inuwar jam'iyyar APC, galibi sun yi hakan ne saboda abin da suka kira gazawar gwamnatin jam'iyyar PDP karkashin jagorancin shugaba Goodluck Jonathan, da kuma tsananin mawuyacin hali da kasar ke ciki a lokacin.
Suna da yakinin cewa shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya, da kishin talakawa da jajircewa wajen aikin kyautata rayuwar jama'a.
Sun kasance da dogon buri na cewa zai warkar da kasar daga matsanancin rashin lafiyarta - kama daga tabarbarewar tsaro, zuwa ga tsananin talauci da raunin sha'anin kula da lafiya da na ilmi da dai sauransu.
To amma bayan wani lokaci sai suka fara jin burinsu ba ya cika, kuma gwamnatin na tafiyar hawainiya abin da ya sa aka rada wa shugaba Buhari lakabin ''Baba Go-Slow''.

Asalin hoton, Buhari Sallau
Mukarraban gwamnati sun rika bai wa 'yan kasar hakuri cewa a yi wa gwamnatin uzuri domin gyaran barnar da aka yi ba zai yiwu a dare daya kamar yadda wasu ke tsammani ba saboda girmanta. Sai dai daga bisani hakurin wasu 'yan kasar ya kure musamman saboda matsin rayuwa da suke ciki.
Dalilin da ya sa 'yan Najeriya suka rika lekawa da dubawa domin fahimtar abin da ya sa shugaba Buhari ya kasa share masu hawaye a kan lokaci kamar yadda suka yi tsammani tun farko.
Sai wasu suka tuna da karin maganar da ke cewa ''Ba a mugun sarki sai mugun bafade.''
Daga nan suka fara nuna yatsa ga makusantan shugaba Buhari suna cewa su ne ke yi wa shugaban tarnaki da hana ruwa gudu, domin su a iya saninsa shugaba Buhari mutumin kirki ne, mai kishin kasa kuma mai son ganin talaka na jin dadi.
Kasancewar marigayi Abba Kyari shi ake jin ya fi kusa da Buhari, sai sukar ta fi karkata wajensa -sukar da ya jure, ya yi ta sha, har zuwa lokacin da Allah Ya karbi ransa.
Ko baya ga zargin kakkange shugaban daga jama'a, wasu rahotanni sun kuma zargi tsohon shugaban ma'aikatan fadar shuagban kasar da karbar rashawa domin bayar da kwangiloli, ko kuma bayar da mukamai a gwamnatin.
Ba a cika jinsa yana mai da martani ga suka ba, sai dai wasu cikin jami'an gwamnati ko masu goyon bayan gwamnati ke kare shi.
Shi kansa shugaba Buhari ya kasance mai kare Abba Kyari daga zargi inda ya bayyana marigayi aminin nasa a matsayin mutum mai kyamar rashawa da kuma yaki da ita haikan.
A jimlace, gwamnatin kan kare salon tafiyarta, tana mai cewa ta kawo ci gaba a kasar a fannoni daban-daban, kama daga inganta aikin noma don wadata kasa da abinci, da tallafa wa talakawa da kuma yaki da cin hanci da rashawa da dai sauransu, kuma cewa tana ci gaba da yin iya kokarinta.
Marigayi sha-yabo

Asalin hoton, Presidency Nigeria
Duk da cewa tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya Malam Abba Kyari ya kasance dankali sha-kushe a lokacin da yake raye kuma yake aiki a gwamnatin Buhari, to amma mutuwarsa ke da wuya sai aka ji mutane daga ciki da wajen gwamnati, da kuma ciki da wajen Najeriya, na ta yabonsa.
Nan take ya zama 'marigayi sha-yabo'.
Kusan galibin mutane da suka yi magana kan rasuwarsa, sun yi masa fatan samun kyakkyawar makoma.
A lokacin jana'izarsa a makabartar da ke Gudu a Abuja babban birnin Najeriya, malamin addinin musulunci da ya jagoranci addu'o'i ga mamacin, kuma ministan sadarwa Sheikh (Dr) Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa "bisa dukkan alamu Abba Kyari ya yi shahada saboda yanayin mutuwarsa."
"Na farko ya rasu a ranar Juma'a, na biyu kuma a cikin yanayin annoba. Bisa koyarwar addinin musulunci, wadannan na daga cikin alamomi da ke nuna cewa mutum ya yi kyakkyawar karshe," in ji Pantami.

Asalin hoton, Twitter/@NGRPrersident

Asalin hoton, Twitter/@NGRPresident

Asalin hoton, Majeeda Studio
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Abba Kyari mutum ne da ya yi zarra, yana mai bayyana shi a matsayin mutumin da ya yi wa dukkan 'yan Najeriya adalci ba tare da nuna bambanci ba.
Ita ma mai dakin shugaban kasar, Aisha Buhari, cikin sakonta na ta'aziyya, ta roki Allah ya sanya marigayin a gidan Aljanna, ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure rashin.
Shi ma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya yi takara, ya kalubalanci shugaba Buhari a zaben 2019, da kuma tsohon shugaban kasa Goodkuck Jonathan wanda Buhari ya kayar a zaben 2015, a sakwanninsu daban-daban duka sun bayyana takaicinsu da rasuwar Abba Kyari tare da yi wa shugaban kasa da iyalan mamacin ta'aziyya.
Hatta mutanen da ke gaba-gaba wajen sukar gwamnatin Buhari wadda a cikinta Abba Kyari ya kasance babban mai ruwa da tsaki, sun nuna jimani kan rasuwarsa tare da yi masa fatan samun makoma ta gari.
Misali, tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode, ya ce ko da yake suna da bambancin ra'ayi, to amma "Abba mutumin kirki ne, mai martaba, kuma aminina ne. Allah Ya ji kansa."
Ita ma babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta bayyana mutuwar Malam Abba a matsayin "abin bakin ciki da takaici' kuma babbar hasara ga Najeriya."
Mai yiwuwa wadannan sakwannin yabo na da nasaba da lamura da dama. Bisa al'adu da addinai da galibin 'yan Afirka ke bi, ba daidai ba ne a rika aibanta mamaci musamman wanda ya fito daga rukunin mutane da ke isar da sakwanninsu kan mutuwar.
Haka zalika Bahaushe na cewa murnar mutuwa murnar banza domin ko ba jima ko ba dade, za ta iske shi ma mai murnar.
Sannan kuma tabbas akwai wadanda suka yi imani tsakani da Allah marigayin mutumin kirki ne, suna kuma kyautata masa zaton shiga Aljanna bisa rahamar Allah.
''Ba a fahimci Abba Kyari ba lokacin da ya ke raye''

Asalin hoton, Buhari Sallau
Dattjijon mai jar dara, mutum ne mai kwarjini da natsuwa. Wadanda suka yi hulda ta kud-da-kud da shi sukan ce ko da yake mutum ne da ba ya son wasa musamman kan abin da ya shafi aiki, to amma yakan dan taba barkwanci daga lokaci zuwa lokaci.
Tsohon dan jarida kuma manajan banki, Malam Abba, ba mutum ne mai yawan magana a bainar jama'a ba musamman lokacin da ya ke rike da mukamin shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya.
Shi dai Abba Kyari har ya mutu ba a cika jin ta bakinsa ba kan zarge-zargen da jama'a da dama ke yi a kansa, watakila saboda yanayinsa na rashin yawan magana a bainar jama'a.
Bisa dukkan alamu kuma, har abada, 'yan Najeriya ba za su ji ta bakinsa kai tsaye ba - damar hakan ta kubuce, kuma ba za ta dawo ba. To amma za a iya ci gaba da sharhi da tsokaci kan rawar da ya taka a mulkin shugaba Buhari wadda aka yi imanin ta shafi rayuwar al'umma da ma makomar Najeriya.
To sai dai kuma, bayan mutuwarsa masu ta'aziyya musamman wadanda suka yi aiki da shi na ta bayyana yanayinsa da kuma yadda suka san shi.

Asalin hoton, Presidency
Da dama suna cewa ba a fahimce shi ba ne, shi ya sa mutane ke ta sukarsa da kuma yadda ya tafiyar da lamuran gwamnati.
Malam Sama'ila Isa Funtua, wani da ya yi aiki tare da marigayin tun shekarun 1980, ya ce mutum ne "mai gaskiya da kokari da rikon amana" da kuma aiki tukuru.
Wasu jami'ai na ganin Abba Kyari ya taka rawa sosai wajen kawo ci gaba a Najeriya.
Gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar ya shaida wa BBC cewa marigayin ya taka rawa wajen shirin gwamnati na taimaka wa manoman Najeriya don bunkasa aikin noma da samar da abinci - daya daga cikin manyan ayyukan raya kasa da gwamnatin Buhari ke alfahari da su.
"Ya kuma taimaka a aikin samar da wutar lantarki da ake yi," in ji Gwamnan na jihar Jigawa.
Alhaji Badaru ya kara da cewa mutane ba su fahimci marigayin ba, domin kuwa duk wanda ka ga sun samu matsala da Abba Kyari to bai 'fuskance shi ba ne'' kuma idan kana so ku bata da shi ''to ka zo da abin da zai cutar da Muhammadu Buhari ko abin da zai cutar da Najeriya.''

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaba Buhari ya ce Abba Kyari ya yi aiki tukuru, ba tare da neman suna ko yi wa kansa kirari ba, babban burinsa shi ne ya tabbatar an kyautata yadda gwamnati ke gudana a Najeriya.
Wani mai gidauniyar tallafa wa marayu da ake kira Future Prowess Islamic Foundation, da ke Maiduguri, Malam Zannah Mustapha, ya ce mutum ne da ba ya so a rika yawan yabonsa.
Da ya ke bayani kan irin gudummuwar da Abba Kyari ya bayar wajen ilmantar da marayu, Zannah ya ce da "Malam Abba na raye kuma ya ji yana yabonsa karara a rediyo kan ayyukansa da mun samu dabani da shi."
Shin mutuwar Abba Kyari za ta sauya salon tafiyar gwamnatin Buhari?
Ganin yadda mutane da dama a ciki da wajen Najeriya suka hakikance kan cewa marigayi Abba Kyari ne ya kasance mai juya akalar gwamnatin Najeriya yadda yake so tun lokacin da aka ba shi mukamin a 2015, tambayar da wasu ke yi ita ce shin ina makomar salon tafiyar gwamnatin Buhari bayan wucewar Malam Abba?
Mutane da dama na ganin Abba Kyari ya bar babban gibi a gwamnatin Najeriya. Shi dai shugaba Buhari yakan musanta zargin cewa wasu 'yan tsiraru da ake kira 'Cabal' da Ingilishi ne, ke juya shi tare da tafiyar da gwamnatin yadda suka ga dama - jigo cikinsu kuma shi ne marigayi Abba Kyari.

Asalin hoton, Twitter/@NGRPresident
Shugaban ya ce babu wani mataki da wani ke sa shi dauka ba tare da ya gamsu cewa shi ne matakin da ya fi dacewa da manufofin gwamnatinsa da muradun kasa ba.
To amma bayanin na shugaba Buhari bai kawar da tunanin da jama'a ke da shi ba, na cewa marigayi Abba Kyari shi ya kasance mai wuka da nama a gwamnatin har zuwa lokacin mutuwarsa.
Ko ma yaya gaskiyar lamarin ta ke, shekaru uku da suka rage na wa'adin mulkin Buhari za su iya bayar da karin haske kan rawar marigayin da tasirinsa da kuma karfin ikonsa a gwamnatin a lokacin da ya ke raye.
Idan tabbas Abba Kyari ne ya kasance mai juya akalar gwamnatin tun daga 2015 zuwa lokacin mutuwarsa, to akwai yiwuwar salon tafiyar gwamnatin ya sauya. Idan kuma ba shi ne ba, to sauya salo sanadiyyar rasuwarsa abu ne mai wuya. To amma babu tabbacin cewa wanda zai gaje shi zai samu karfin iko da yardar shugaba Buhari irin nasa.
Mai sharhi kan lamuran siyasa, Dr Abubakar Kari, ya ce tun da mukamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati ba mukami ne da kundin tsarin mulkin kasa ya zayyana ikon da ke tattare da shi ba, to shugaban kasa shi ne mai ba shi iya hurumin aikinsa da karfin iko gwargwadon yadda shugaban kasar ya ga ya dace.
Mai sharhi kan siyasar ya ce muddin shugaba Buhari ya ci gaba kan tsarinsa na cewa duk wani minista ko jami'in gwamnati dole ya bi ta ofishin shugaban ma'aikata kafin ya samu wani abu ko kuma ya gana da shi kamar yadda aka gani a zamanin Abba Kyari, to ofishin shugaban ma'aikatan zai iya ci gaba da kasancewa mai dimbin iko da tasiri a gwamnati.
Haka kuma manazarta siyasa na ganin, irin mutumin da shugaba Buhari zai bai wa mukamin shugaban ma'aikatan fadarsa da yadda tafiyar gwamnatin za ta kasance, ka iya yin tasiri ga jam'iyyar APC mai mulki a babban zabe na 2023.
A halin da ake ciki dai Malam Abba Kyari ya tafi, kalubalen rayuwa kuma ya rage ga wadanda ke raye.











