Yadda coronavirus ta shiga fadar shugaban Najeriya Buhari

Muhammadu Buhari da Abba Kyari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Abba Kyari shi ne shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa
Lokacin karatu: Minti 3

Labarin da ya bayyana cewa shugaban ma'aikata a fadar shugaban Najeriya, Abba Kyari, ya kamu da coronavirus ya ja hankalin 'yan kasar sosai saboda girman mukaminsa.

Majiyoyi a fadar shugaban Najeriya ta Aso Rock da ke Abuja da dama sun bayyana cewa sakamakon gwajin cutar da aka yi wa Malam Abba Kyari ya nuna cewa ya harbu da cutar numfashi ta coronavirus.

Duk da yake ya zuwa yanzu, hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasar ta sanar da mutum sama da 40 da suka kamu da cutar, amma Abba Kyari shi ne babban jami'in gwamnatin kasar da ya harbu da covid-19.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ambaci sunansa ba saboda tsarin ta na rashin ambatar sunan wadanda suka kamu da cutar, sannan gwamnatin Najeriya bata tabbatar ba a hukumance duk da tuntubar da BBC ta yi wa mutane daba-daban a fadar shugaban kasar.

Rahotanni na cewa shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasar ya kai ziyarar aiki kasar Jamus, ranar 7 ga watan Maris kuma ya koma Najeriya ranar 14 ga watan na Maris, ko da yake a lokacin bai nuna alamun rashin lafiya ba.

Sai dai masu sharhi na ganin ya kamata tun lokacin da ya koma Najeriya ya killace kansa domin yin biyayya ga umarnin da gwamnatin kasar ta yi cewa duk mutumin da ya koma kasar, to ya killace kansa tsawon mako biyu kafin ya soma gana wa da jama'a.

Hasalima, wasu rahotanni sun ce tun lokacin da ya koma gida, Abba Kyari ya halarci taruka daban-daban kan matakin da gwamnati take dauka domin shawo kan cutar ta COVID-19.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Ko da a makon jiya mai dakin shugaban kasar, Aisha Buhari, ta sanar da cewa 'yarta ta killace kanta bayan komawarta Najeriya daga Birtaniya.

Ta ce 'yar tata, wadda bata ambaci sunata ba, ta killace kan nata ne saboda shawarar da hukumomin lafiyar kasar suka bayar.

Tuni dai 'yan kasar, ciki har da manyan 'yan siyasa da jami'an gwamnati suka soma taya shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar alhini.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter Alhaji Atiku Abubakar, wanda shi ma dansa ya kamu da cutar, ya yi addu'ar samun sauki ga Abba Kyari.

"Ina yin addu'a ga shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari. Allah ya kare mu ga baki daya, kuma ya ba shi lafiya," in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Wacce barazana hakan zai yi ga sauran jama'a?

Abba Kyari ya gana da Yahaya Bello

Asalin hoton, Kogi government

Bayanan hoto, Abba Kyari ya gana da Yahaya Bello a Lokoja

Rahotanni sun ce tun bayar komawar Abba Kyari Najeriya, ya gana da manyan jami'an gwamnati da gwamnoni da 'yan kasuwa da dama.

A makon jiya ne, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya jagoranci tawagar da ta je Lokoja, babban birnin jihar Kogi, domin mika sakon ta'aziyyar Shugaba Buhari ga Gwamna Yahaya Bello, wanda mahaifiyarsa ta rasu kwanakin baya.

Kazalika, wasu rahotanni sun ce Abba Kyari ya halarci wani daurin aure a karshen makon jiya a Abuja, babban birnin kasar, wanda manyan mutane irin su Aliko Dangote da Gwamna Aminu Bello Masari suka je, kuma sun zauna kurkusa da juna.

Yaya tsarin aikinsa yake?

A matsayinsa na shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Malam Abba Kyara yana da ruwa da tsaki a kan kusan komai da ya shafi shugaban kasar.

Shi ne mutumin da yake tsara komai game da ayyukan shugaban kasar, sannan yakan gana da akalla mutum 20 a kowacce rana, a cewar wasu ma'aikatan fadar ta shugaban Najeriya.

Wani dan jarida da ke dauko rahotanni a fadar shugaban Najeriya, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya shaida wa BBC cewa a kullum Abba Kyari yana gana wa da Shugaba Buhari akalla sau hudu.

Kazalika yana ganawa da gwamnoni da ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati wadanda ke son gana wa da shugaban kasa.

Rahotanni sun ce ganin irin mutanen da ke gana wa da abba Kyari a kullum, wasu daga cikinsu na fuskantar hadarin kamuwa da cutar, musamman wadanda suka yi musabaha ko kuma zama kurkusa da shi.

Tuni dai rahotanni suka ce da yawa daga ma'aikatan fadar shugaban kasar sun killace kansu.

Karin labarai masu alaka