Fatawar Malaman addinin Musulunci a Najeriya kan coronavirus
A yayin da cutar covid-19 ke ci gaba da yaduwa a duniya, malaman addinin musulunci a Najeriya sun yi tsakani kan cutar. Ga abin da wasu daga cikinsu suka shaida wa BBC Hausa:
A yi biyayya ga umarnin hukumomi - Sheikh Ahmad Gumi

Asalin hoton, Facebook/Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Ahmad Abubakar Mahmud Gumi: "Ya kamata shugabanni su tara masana su yi bayani kan wannan batu na coronavirus. Don haka idan masana suka bai wa shugabanni shawara cewa a daina ko da sallah ce a cikin jama'a, to wajibi ne a daina. Wannan ita ce koyarwar manzon Allah. Don haka muna kira ga al'umma su yi biyayya ga dukkan umarnin da suka bayar kamar wanke hannu akai-akai da amfani da sinadarin kashe kwayoyin cuta da kuma dana musabaha."
A daina shiga cikin taro wanda ake cunkuso - Sheikh Dahiru Bauchi
"Abin da zan fada wa al'uma su saurari abin da likitoci suke fada; suke bayar da nasiha ko wanke hannu ko hana gaisawa da musabaha da sauran abubuwa wadanda likitoci suka bayar da umarni duka sai a bi musu domin Allah ya ce 'wanda ya san abu da wanda bai san shi ba ba za su zama dai-dai ba. To, harkar da ta shafi ciwo irin wannan, su likitoci harkokinsu ne su suka san abin. Idan sun bayar da nasiha sai a bi musu -- yawan wanke hannu ko kuma dakatawa da gaisawa hannu da hannu ko kuma shiga cikin taro wanda ake cunkuso."
Coronaviru ba sabon abu ba ne - Sheikh Aminu Daurawa

Asalin hoton, Facebook/ Mal.Aminu Ibrahim Daurawa
"An dade ana gamuwa da ibtila'i da jarrabawa a fadin duniya, kwalara da Annoba da yaduwar cutaka ya dade yana addabar duniya, kuma ana yi masa fassara iri- iri, kowa gwargwadon abin da yake dauke da shi na akida ko hankali ko ilmi ko al'ada ko surkulle.
Amma mu a mahanga ta addini muna daukar wadannan a matsayin jarrabawa da jan kunne da Allah yake yi wa mutane domin su saduda, su sallamawa Allah, su yadda wannan duniya akwai me ita, kuma yana da iko akanta kuma zai Iya tashin ta duk sadda yaga dama...
Mu yi abubuwa biyar:
Na daya yadda da kaddara mai dadi da mara dadi duk daga Allah ne
Mu dauki matakan kare kai yadda jamian kiwan lafiya suke fada
Mu dukufa da tuba da istigfari da komawa ga Allah, domin ya yaye mana wananan Annoba, da yawaita zikri da addua.
Duk musulmin da ya mutu yayi shahada.
Kada mu shiga inda Annoba take, kada kuma mu fita daga inda ake yi har sai an tabbatar da bamu dauka ba."
A bi shawarwarin likitoci - Sheik Yaqub Yahya Katsina

Asalin hoton, Sheik yaqub yahya katsina
"Ba zai yiwu ya zama ba abin dokar Allah ba kuma dokar da mutane suka yarda suka yi wa kansu kuma ba abi sannan kuma ace zaa samu yadda akeso.Saboda haka kar acire hannun Allah aciki, ace dalili kaza ne, sannan abi shawarwarin likitoci; duk shawarwarin da likitocin suka bada da masana akan wannan fanni na kiwon lafiya, to abi wadannan shawarwarin kuma a tsare su.
Sannan kuma ayi kokari ya zamana kowa addininsa - kirista ko musulmi - ya koma wurin Allah ya nemi gafara ya kuma yi addu'a Allah ya yaye wa duniya wannan bala'i daya tunkaro ta wanda kuma baasan ina aka dosa ba."












