Gwamnan Bauchi Bala Kaura ya kamu da coronavirus

Asalin hoton, Bauchi Gov
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya kamu da coronavirus bayan da sakamakon gwajinsa ya fito.
A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar mai dauke da sa hannun babban mai bai wa gwamnan shawara kan yada labarai Mukhtar M Gidado, a ranar Talata.

Asalin hoton, Bauchi
BBC ta samu tabbacin haka daga wajen wani makusancin gwamnan.
Sanarwar ta ce daga cikin mutum shida na jami'an gwamnatin Bauchin da aka yi wa gwajin, na gwamnan ne kawai ya nuna yana dauke da cutar.


Dama tun a ranar Litinin ne gwamnatin jihar ta sanar da cewa gwamnan ya killace kansa tun bayan hada jirgi da ya yi da dan gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda ya kamu da cutar coronavirus.
Mai magana da yawunsa, Ladan Salihu ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ladan ya ce "mun hau jirgi daya da dan gidan na Atiku daga Lagos zuwa Abuja, inda suka yi musabiha hannu da hannu. Tuni aka yi wa gwamna da mu 'yan tawagarsa gwaji. Muna fatan sakamakon gwajin zai yi kyau."
Kwamishinan ilimi na jihar Bauchin ya shaida wa BBC cewa a yanzu haka an umarci dukkan 'yan majalisar zartarwa gwamnan da su killace kansu na tsawon kwana 14.











