Abubuwan da kuke son sani kan Zakkar Fid-da-kai

Asalin hoton, Facebook/Maraya
Malamai sun ce bisa nassi an fara Zakkar Fidda-kai bayan hijirar Annabi Muhammad SAW da shekara biyu, wato a shekarar da aka wajabta Azumin Ramadan, saboda haka Sunna ce mai karfi da ke da nufin wanzar da zaman lafiya tsakanin al'ummar musulmai.
Tasirin Zakkar Fidda-kai guda 3 tsakanin musulmi
BBC ta tattauna da wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Kaduna, Malam Halliru Maraya kan Zakkar Fidda-kai da tasirinta a tsakanin musulmai.
Malamin ya lissafa wasu abubuwa guda uku a matsayin tasirin da Zakkar Fidda-kai ke yi a tsakanin musulmi:
- Tabbatar da wadatar abinci tsakanin musulmai, ko wanne musulmi ya yi sallah da abincin da zai ci da iyalinsa.
- Ana amfani da Zakkar Fidda-kai wajen kankare zunuban da musulmi ya aikata cikin azumi, wadanda ba su ɓata masa azuminsa ba amma sun rage masa lada.
- Tana kara zumunci da soyayyar juna tsakanin musulamai.
Yadda ake fitar da ita
Sheikh Halliru Maraya ya ce ana fitar da Zakkar da dukkan wani nau'in abinci da al'ummar da mutum ke rayuwa cikinta ke ci, musamman tsaka-tsakin abincin da aka fi ci, ko kuma abincin da suka fi ci gwargwadon hali.
"Idan wurin da mutum yake garin kwaki ake ci to shi ya kamata ya yi zakkar da shi, idan dabino suke ci da shi za su yi."
Ya kara da cewa an fi son abin da kake ci ka fitar da zakkar da shi, amma ba "wajibi ba ne don mutum yana cin shinkafa a gidansa ace sai ya yi zakkar da ita," in ji Sheikh Halliru.

Wadanda ya kamata su fitar da ita
Idan mutum yana da wadata zai fitar a kansa ya kuma fitar wa da wadanda ke karkashinsa wato mutanen da yake ciyar da su.
"Zakkar tana kan dukkan musulmin da yake ya wadatu, wadata ta bangaren abincin da za a ci da kuma wadata ta bangaren kudaden da zai iya bayarwa a sai abincin da su.
Tana kan dukkan musulmi, babu mace babu namiji, babu babba babu yaro, ana fitar wa ga yaran da suke da kudi.
Wasu yaran marayu ne ana iya fitar musu cikin duniyarsu, wasu kuma irin kyautar da ake musu ko kuma wadanda iyayensu ke buɗe musu asusun banki, duk za a fidda zakar cikin kudinsu.
Idan 'ya'yan mutum maza sun balaga kuma lafiyarsu kalau to zakkarsu ta sauka daga kan mahaifansu. Amma idan ya ce zai ci gaba da fitar musu duk da haka, to babu laifi a Musulince.
Idan kuma mata ne 'ya'yan mutum ko sun balaga zai ci gaba da fitar musu har sai sunyi aure sun yi tarayya da mazajensu, a lokacin ne zakkar take sauka daga kan mahaifinsu."
Lokacin da ake farawa da na kammalawa
Sheikh Maraya ya ce "kokacin fara fitar da zakkar ya sha banban daga mazhaba zuwa mazhaba a musulunce, kamar a wajen Abu Hanifa kafin Ramadan ma mutum zai iya fitar da zakkar.
A mazhabar Shafi'iyya da zarar an ga watan Ramadan ko a ranar 1 ga watan za a iya ba da ita.
Malikiyya da Hambaliyya suna ganin sai ya rage kwana daya ko biyu azumi ya kare sannan za a fara raba zakkar. Saboda daya daga cikin manufofinta shi ne musulmai su yi bikin sallah da abinci wadatacce a gidajensu."
Dangane kuma da wajabcin Zakkar ta Fidda-kai Malam Halliru Maraya ya ce "wajibcinta yana farawa ne daga lokacin da rana ta faɗi a azumin karshe na watan Ramadana.
Da an dawo daga sallar Idi to lokacin Zakkar Fidda-kai ya fita, komai aka ba da bayan nan daidai da sadaka yake. Wannan na cikin dalilan da yasa ake jinkirta Sallar Idi domin mutune su samu su fitar da zakkar kan lokaci ya kure.
Mizanin da ake bayarwa
Sheikh Halliru Maraya ya ce "mizanin Zakkar Fidda-kai shi ne Sa'i daya ga kowanne mutum. Sa'i daya wato mudu hudu ko kuma kwatankwacin nauyin kilogiram biyu da rabi na shinkafa, shi ne abin da ake so a fitar wa kowanne mutum daya a matsayin Zakkar Fidda kai.
Amma duk abin da aka bayar kasa da haka sunan shi sadaka. Akan bayar da kudin da za su iya sayan abincin da zai yi kimar kilogiram biyu da rabi. Amma domin samun cikakken lada mutum sai ya ba da kudin a sai abincin a yi masa zakkar."

Zakkar Fidda-kai a shekarar 2020 ta zo a wani yanayi na kunci da jama'a suka kasance a ciki sakamakon matakan da gwamnatoci ke dauka a kokarinsu na dakile bazuwar annobar korona.
Hakan ne ma ya sa wasu malaman ke ganin ba laifi idan masu hali suka kara kyautatawa kan abin da Shari'a ta ce a bayar.












