An kama Félicien Kabuga a Faransa da ake zargin ɗaukar nauyin kisan kiyashi a Rwanda

Asalin hoton, US state department
An kama Félicien Kabuga a Paris, ɗaya daga cikin waɗanda ake nema ruwa jallo kan kisan kiyashi a Rwanda, kamar yadda ma'aikatar shari'a ta Faransa ta sanar.
An kama Mista Kabuga a Asnières-sur-Seine, inda yake rayuwa bayan ya ɓoye sunansa.
Kotun duniya kan manyan laifuka a Rwanda ta tuhumi Kabuga mai shekara 84 da laifin kisan ƙare dangi da kuma keta haƙƙin bil'adama.
Ana zargin, shi ne babban mai tallafa wa ƴan hutu waɗanda suka kashe mutum 800,000 a 1994.
Sun kasance masu kai wa ƴan kabilar Tutsi tsiraru hare-hare, da kuma abokan adawarsu na siyasa.
Amurka ta yi alkawalin bayar da tukuicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya bayar da bayanan da ya kai ga kama Mista Kabuga

Wane ne Félicien Kabuga?
Daga Will Ross, Editan BBC na Afirka
Dan kasuwa ne daga kabilar Hutu wanda ake zargi a matsayin babban mai bayar da tallafin kuɗi ga ƙungiyoyin da suka aikata kisan kiyashin Rwanda.
Shi ne ya samar da kafar yaɗa labarai ta (RTLM), da ke ƙarfafa wa mutane guiwa don bincikowa da kuma kashe duk wani ɗan ƙabilar Tutsi da suka samu.
An kama shi ne can wajen garin Paris, yana amfani da wani sunan ƙarya.
Shekaru da dama, ana tunanin Félicien Kabuga yana rayuwa ne a cikin Kenya, inda ake zargin manyan ƴan siyasa da hana ƙokarin kama shi.
Sama da shekaru 25 bayan kisan kiyashi, zai gurfana gaban kotun duniya.

Yadda aka gano shi
Masu shigar da ƙara a Faransa da ƴan sanda sun ce Mista Kabuga yana rayuwa ne da sunan ƙarya a wani gida tare da ƴaƴansa.
An kama shi ne misalin ƙarfe 5:30 na safe (03:30 GMT) a ranar Asabar wanda babban shigar da ƙara da ke kula da shari'ar laifukan da aka aikata a Rwanda da tsohuwar Yugoslavia a kotun Hague ya kira babban bincike da samame da aka gudanar a wurare da dama.
"Kama Félicien Kabuga a yau, tunatarwa ce kan waɗanda ke da hannu a kisan kiyashi za su fuskanci hukunci, shekru 26 bayan aikata laifukansu," kamar yadda Serge Brammertz ya fada a cikin wata sanarwa..
Ya ƙara da cewa "kama Kabuga ya nuna cewa za a yi nasara idan an samu goyon bayan ƙasashen duniya."
Mr Brammertz ya bayyana godiyarsa ga Faransa, amma kuma ya ce ƙasashen Rwanda da Belgium da Jamus da Netherlands da Austria da Luxemburg da Switzerland da Amuka da kuma hukumomin ƴan sanda da Europol da Interpol duk sun taka muhimmiyar rawa.
Bayan kammala bin matakan da suka dade ƙarƙashin dokokin Faransa, ana sa ran Mista Kabuga za a miƙa shi zuwa inda zai fuskanci shari'a.
A 1997 aka tuhume shi da aikata laifukan kisan kiyashi guda bakwai.











