Coronavirus: An samu raguwar yaduwar sakonni a WhatsApp

WhatsApp ya dauki wasu sabbin matakan dakile yada labaran karya a farkon watan Afrilu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, WhatsApp ya dauki wasu sabbin matakan dakile yada labaran karya a farkon watan Afrilu

WhatsApp ya ce ya ga raguwar sakonnin da ake turawa da kaso 70 cikin 100 - irin na karyar nan da ake yadawa kan cutar korona.

Hukumar Lafiyar Ta Duniya ta ce labaran karyar da ake yadawa kan cutar abu ne mara kyau.

Mako biyu da suka gabata, WhatsApp ya hana mutane tura sako daya ga abokansu sau biyar a jere ko tura shi sama da sau daya a zauruka a daban-daban.

Amma masana sun ce duk da haka akwai bukatar a kara daukar matakai kan yaki da labaran bogi.

"WhatsApp na iya kokarinsa wajen dakile yada irin wadannan sakonni," in ji mai magana da yawun manhajar.

"Wannan sauyin na taimakawa WhatsApp na zama dandalin tattauanwa tsakanin daidaiku da kuma abokai."

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Sakonnin karya na yaduwa cikin gaggawa?

Daga Marianna Spring, wata kwararriya wakiliya kan yada labaran karya

WhatsApp sai da ya zama wani dandalin yada labaran bogi a lokacin wannan annoba.

Abokai da 'yan uwa da ke nuna damuwa kan cutar na amfani da gurup wajen tura sakonnin da suka shafi shawarwarin masana ko kuma hasashe kan shirin gwamnatoci, "ko da ta baci"| za a iya mafani da su.

WhatsApp da kuma sauran dandalin sada zumunta na da wuyar bibiyar al'amura kamar Facebook, Twitter ko kuma YouTube - mu mun dogara ne kan korafin da mutane ke yi mana kan sakonni.

Amma da alamun mun tsallake matakin farko na bazuwar labaran karya ta dandalin WhatsApp.

Yayin da sakonnin da kake samu uka ne akwai tankoki a kan titi kuma ka jira ba ka gansu ba, dole za ka fara shakku a kansu.

Wannan ba ya nufin ba ma ganin sauran labaran bogin wadanda ake yadawa kan sassauta dokar kulle - to mene ne zai faru gaba.

Presentational grey line

Shugaban cibiyar............ Imaran Ahmed ya shaida wa BBC cewa: ''Akwai bukatar kara zage damtse game da kafofin sada zumunta kamar su WhatsApp.

"Akwai dumbin labaran karya a wannan kafa ta WhatsApp.

"Wannan kaso 70 cikin 100 na sakonnin da aka samu raguwarsu, na nuna rikita-rikitar da ke da akwai yayin da gano labaran karya ke da matukar amfani."

Wanne tsarin lissafi suke amfani da shi?

"A lokacin da mutane ba sa iya haduwa fuska da fuska, an fi yada labaran karya ne ta kafafen sada zumunta"

Presentational grey line