Coronavirus: Shawarwari kan yadda za a yi azumi a cikin kulle

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Abuja Bureau
Yayin azumin watan Ramadana na bana, intanet ce za ta zama kusan babbar abokiyar hulda, duk da cewa malamai na gargadar masu azumi a kan yin hakan a baya.
"Wannan azumin daban ne da ragowar (wadanda aka yi a baya), saboda haka dole ne a samu sauyin abubuwa" a cewar Dr Umar Bawa, malami a sashen koyar da addinin Musulunci a Jami'ar Bayero ta Kano.
Ko ba a fada ba za ku iya hasaso dalilin da ya jawo hakan - zaman gida da kusan dukkan al'ummar duniya ke yi sakamakon yakin da ake yi da yaduwar cutar korona.
Wannan karon har da kamfanin Facebook a shirye-shiryen azumin, inda ya hada kai da Basma Khalifa da Mabdulle, wasu 'yan Birtaniya, da wani ma'aikacin BBC mai suna Mim Shaikh.
Cikin wani shiri mai lakabin #RamadanTogether, za su rika samar da bidiyo kan yadda rayuwar azumi take yayin zaman gida.
Wannan dalili ne ya sa muka duba muku shawarwari da za su taimaka muku wurin gudanar da azumi yayin da ake zaune a gida.

Shawara kashi na farko; Daga Imam Murtadha Gusau, wani Malamin Addinin Musulunci a Najeriya
Yin azumi a kulle a gida na iya zama abin kirki, amma sai idan mun so hakan. Me ya sa? Don samun kusanci da Allah, da tabbatar da yin mai kyau da barin marar kyau, mu'amala da masu karamin karfi da yin godiya a kai a kai.
Duk shekara, kowane Musulmi na burin fahimtar Al-Kur'ani, ya fahimci sakonsa da kuma sanin wanda ya zo da shi (Annabi Muhammadu, tsira da aminci su tabbata a gare shi) sannan fiye da komai, Musulmi ya kamu da soyayyar wanda Ya aiko da Al-Kur'anin (Allah mai Girma da Daukaka).
Alaka ta musamman da ke tsakanin Watan Ramalana da Al-Kur'ani Mai Tsarki ba boyayyen abu ba ne, don kuwa a wannan watan ne aka saukar da Littafin Mai Tsarki. Allah mai Girma da Daukaka yana cewa:
"Watan Ramalana shi ne watan da aka saukar da Al-Kur'ani don ya zama hanyar shiriya ga dan Adam." [Al-Kur'ani, 2:186]

Asalin hoton, Getty Images
Kowa, babba da yaro, na iya amfani da wannan lokaci don yin wannan aikin ibada mai albarka.
Yara na iya fara koyon karatun Al-Kur'ani; wadanda suka iya karatun na iya fara koyon Harshen Larabci; wadanda suka iya Larabci sama-sama, a yanzu za su iya fara koyon fassara da Tafsiri (wato bayani kana bin da Al-Kur'ani ya kunsa)
Daga karshe, akwai wani bangare na Watan Ramalana da ake mayar da hankali kansa a goman karshe na watan, ana kiransa Ittikafi. Wannan dokar zama a gidan ta ba mu damar yin Ittikafi a gidajenmu.
Don haka, me zai hana mu yi amfani da wannan dama da Allah Ya ba mu, mu fahimci yadda ainihin Ittikafi yake.

Karin labaran da za ku so ku karanta

Tsara lokaci
Lokaci abu ne mai muhimmanci kuma tsara yadda za a kashe shi ma yana da muhimmancin gaske, musamman ganin cewa azumin kwana 29 ko 30 ne kacal.
Zaman gida ka iya rudar mutum ya yi tunanin cewa yana da lokaci mai yawa alhalin hannun agogo ba daina tafiya ya yi ba.
Malam Dr Umar Bawa, Malami a Sashen Koyar Da Addinin Musulunci na Jami'ar Bayero, ya ce abin da mutum ya kamata ya fara yi shi ne ya tsara lokacinsa.
"Ya tsara ta yadda ba zai tozarta lokacinsa ba a kan wasu abubuwa marasa muhimmanci. Ya yi abubuwa da za su kusanta shi ga Allah.

'Sallolin nafila a gida sun fi lada'
Mutane kan yi tururuwa zuwa masallatai a duk lokacin da aka ji kiran sallah da kuma sallolin nafila kamar asham ko tarawihi da kuma kiyamullaili.
Sai dai Malam Dr Umar Bawa ya ce mutane za su iya yin sallolinsu a gida, kuma da ma sallar nafila a gida ta fi lada.
"Annabi ya ce sallar da ta fi falala ga mutum ita ce wadda ya yi a gidansa indai ba ta farilla ba ce," a cewar Umar Bawa.

Asalin hoton, Getty Images
Kazalika, Malam Hussain Zakariyya, Limamin Masallacin Banex da ke Abuja, ya jaddada wannan magana da cewa Allah zai bai wa mutum cikakken ladansa idan ya yi sallarsa a gida saboda dalili mai karfi.
"Musulunci ya tanadi cewa duk ibadar da mutum yake yi - ta dukiya ko ta karfi ko ta harshe - sai wani abu ya sa ba zai iya yi ba saboda rashin lafiya ko tsufa ko tsoro, to Allah zai ba shi ladan wannan ibadar a duk inda yake.
"Amma kamar Tahajjud (kiyamallaili), wannan a gida ake yi ba sai an zo masallaci an hadu ba. Yin sallar farilla a gida a lokacin annoba ya fi lada."
Shi kuma Malam Umar ya kara da cewa "Idan mutane suka fita sallah suka dauko cutar suka yada wa iyalinsu Allah ba zai kyale su ba".

'Taimaka wa mutane har gida'
Malam Hussain Zakariyya ya ce a da a kan bi masallatai domin raba kayayyakin abinci na bude-baki, amma yanzu saboda yanayi hakan ba za ta samu ba.
A saboda haka ne malam ya ce bai wa mutane tallafi a gidajensu ya fi lada sama da kai wa masallatai.
"Gara ka kai wa mutum tallafi gidansa da ka kai masallaci a dafa a bayar, hakan ya fi lada domin ba a son mutum ya fito rokon abin da zai ci."

'Babu ruwan azumi da korona'
Masana harkar lafiya kan ce shan ruwa da yawa da zama a daki mai cike da iska ka iya taimaka wa mai cutar korona yayin da yake jinya.

Asalin hoton, Getty Images
Babu mamaki saboda cutar tana da alaka sosai da numfashi sannan kuma makogwaro ma kafar numfashi ce.
Sai dai Malam Umar Bawa ya ce hakan ba ya nufin cewa wanda yake azumi yana cikin hatsarin kamuwa da cutar korona ba ne.
Ya ce: "Rashin shan ruwa ba ya nufin za a kamu da cutar duk da cewa likitoci sun ce idan makogwaro yana bushewa akwai damuwa.
"Amma duk lokacin da mutum ya ji cewa bushewar makogwaron za ta iya kai shi ga cutuwa, to da ma ai Allah bai dora wa mutane abin da za su cutar da kansu ba. Wanda yake da lafiyarsa garau wajibi ne ya yi azuminsa."

Karin labarai masu alaka












