Coronavirus: 'Yan sanda sun kama matasa masu kwallo a Kano

Asalin hoton, Police
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta cafke da tsare 'yan kwallon kafa 30 a birnin Kano da ke yawo unguwa-unguwa domin buga tamaula da sunan gasa, duk kuwa da dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta kafa.
Kakakin rundunar Abdullahi Haruna ya ce an kama matasan ne a yankin karamar Hukumar Dala da ke birnin Kano, inda suka je domin taka leda.
"Za mu tuhume su da laifin karya dokar hana zirga-zirga a gaban kuliya inda za su kare kansu."
A 'yan kwanakin nan ne dai wani bidiyo da ke nuna wani cincirindon matasa ke kallon 'yan kwallo a wani makeken fili a birnin na Kano.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook
An dai ce a yayin da jihar ta fara aiwatar da dokar kulle, matasan suka fito da gasar kwallon kafa da suka yi wa lakabi da Coronavirus Cup.
Yanzu haka jihar Kano na da adadin da ya kai 73 na masu dauke da cutar korona, baya da ga rahotanni da ke nuna samun yawan mace-mace a birnin.







