An sassauta dokar hana fita a Kano don Azumi

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Nan za mu dakatar da kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu zuwa gobe inda za mu ci gaba da kawo rahotanni da labarai kai-tsaye.

    Mu kwana lafiya.

  2. Gwamnati za ta yi bincike kan yawan mace-mace a Kano

    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan yawan mace-macen da aka samu a jihar Kano.

    Ministan lafiya na Najeriya Dr Osagie Ehanire ya bayyana wa taron manema labarai da ya saba yi kan matakan da ake dauka kan cutar korona cewa babban likita a bangaren kula lafiyar al'umma na jihar Kano zai jagoranci binciken domin gano musabbabin mace-macen a jihar.

    Ya kuma yi gargadi ga masu sayar da magani da asibitoci masu zaman kansu su guje wa kokarin kula da masu dauke da cutar korona idan kuma aka gano su za a kwace lasisinsu

    Ministan ya ce duk asibitin da ke son kula da majinyatan cutar korona sai sun nemi izini daga ma'aikatar lafiya a jihohinsu idan har sun cika sharuddan matakan yaki da cututtuka masu yaduwa.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  3. Za a baza sojoji don hana fita a Afirka ta kudu

    Afirka ta Kudu na shirin baza sojojinta sama da dubu saba'in domin tabbatar da dokar hana fita da gwamnati ta kafa a fadin kasar don dakile yaduwar cutar korona.

    Tun kafa dokar a watan da ya gabata, jami'an tsaro ke kokarin ganin mutane sun kiyaye dokar musamman a biranen da ke da cunkuso, tare da haramta sayar da barasa.

    Ministan tsaron kasar Nosiviwe Mapisa-Nqakula ya ce yadda cutar ke kara yaduwa, shi zai tilasta daukar matakin amfani da soji da ba a taba gani ba a Afirka ta kudu.

  4. Gareth Bale ya bayar da tallafin £500,000

    Dan wasan kwallon kafa na Wales da iyalinsa sun bayar da tallafin fam £500,000 ga hukumomin lafiya a Cardiff da kuma cibiyar agaji ta jami'ar Vale.

    Za a yi amfani da kudin domin samar da wasu abubuwan bukata ga jami'an lafiya da kuma majinyatan cutar korona

    Gareth Bale dan wasan Real Madrid shi ne kaftin din tawagar Wales

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Gareth Bale dan wasan Real Madrid shi ne kaftin din tawagar Wales
  5. Coronavirus ta kashe fiye da mutum 25,000 a Italiya

    Yawan wadanda cutar korona ta kashe a Italiya yanzu sun zarta mutum 25,000.

    Sabbin alkalumman da hukumomin Italiya suka fitar sun nuna cewa cutar ta kashe mutum 437 tsakanin sa'a 24, inda yawan wadanda cutar ta kashe a yanzu suka kai 25,085.

    Sai dai an samu raguwar yawan msu kamuwa da cutar a rana daya inda mutum 107,699 zuwa 107,709 a ranar Talata.

    Italiya ce ta biyu da cutar ta fi yin kisa bayan Amurka

  6. Cutar korona ta kashe mutum daya a Borno

    Mataimakin gwamnan Borno

    Asalin hoton, @GovBorno

    Gwamnatin Borno ta ce gwaji ya tabbatar mutum 9 na dauke da cutar korona a jihar, yayin da kuma cutar ta kashe mutum daya.

    Mataimakin gwamnan jihar Umar Kadafur da ke jagorantar kwamitin yaki da cutar ya shaida wa taron manema labarai cewa gwajin da aka gudanar na mutum 64, ya tabbatar da mutum 50 ba su dauke da cutar, amma kuma ana jiran sakamakon gwaji na mutum 5.

    Ya kuma ce ana jiran sakamakon gwajin da aka gudanar na mutum 11 a Pulka inda cutar ta fara bulla a jihar

    Mataimakin gwamnan ya ce a cibiyar killace masu korona mutum daya ya mutu wanda gwaji ya tabbatar da yana dauke da cutar korona a Gombe bayan ya dawo daga Legas.

    Tuni gwamnatin Borno ta sanar kafa dokar hana fita ta tsawon mako biyu wacce za ta fara aiki a daga karfe 10:30 na daren Laraba.

  7. Labarai da dumi-dumi, An sassauta dokar hana fita a Kano

    Gwamnatin Jihar Kano ta sassauta dokar hana fita zuwa tsawon yini daya, wadda ta saka saboda dakile yaduwar cutar korona a jihar.

    An bai wa mutane damar fita daga gidajensu daga karfe 6 na safiyar Alhamis zuwa karfe 12 na dare.

    Mataimakin gwamna kuma shugaban kwamitin da ke yaki da yaduwar cutar a Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ne ya sanar da hakan, inda ya ce an dauki matakin ne domin bai wa al'umma damar yin shirye-shiryen azumin watan Ramadana da ke tafe.

    Tun a ranar Alhamis da ta gabata ne aka saka dokar hana fita a Jihar Kano ta mako guda bayan an samu bullar cutar korona a jihar.

    Ya zuwa yanzu Kano na da mutum 73 da suka harbu da cutar, inda daya daga cikinsu ya mutu.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  8. Za a dauki lokaci ana fama da cutar korona - WHO

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za a ci gaba da fama da cutar korona a duniya na tsawon lokaci.

    Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya saba yi kan annobar a duniya.

    A cikin jawabinsa ya ce ya tabbatar da cewa yanzu kusan mutum miliyan biyu da rabi ke dauke da cutar korona a duniya, kuma sama da mutum 160,000 cutar ta kashe.

    Ya ce yanzu an fara samun saukin cutar a yammacin Turai, amma a Afirka da tsakiya da kudancin Amurka da gabashin Turai cutar kara bazuwa ta ke.

    Ya ce har yanzu cutar na da ban tsaro, amma irin matakan da aka dauka na hana fita da hana taron jama'a ya taimaka wajen dakile bazuwar cutar a kasashe da dama

    edros Adhanom Ghebreyesus

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Labarai da dumi-dumi, Karin mutum 759 sun mutu a Birtaniya

    Cutar korona ta yi ajalin wasu mutum 759 da ke jinya a asibitocin Birtaniya zuwa karfe 5:00 na ranar Talata, a cewar alkaluman gwamnati na baya-bayan nan.

    Yanzu adadin ya kai 18,100 jumilla.

    Kazalika babu wadanda suka mutu a gida ko kuma wuraren kula da gajiyayyu a cikin adadin.

    A Ingila kuwa, mutum 665 ne suka mutu a asibiti. Hukumar NHS ta ce jumillar adadin ya kai 16,272.

  10. Cutar korona na ci gaba da 'tagayyara tattalin arzikin Somalia'

    Somalia

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan kudi na kasar Somalia ya shaida wa BBC cewa cutar korona na ci gaba da tagayyara tattalin arzikin kasar.

    Abdirahman Duale Beyle ya ce kudin da 'yan kasar mazauna kasashen waje ke aikawa gida ya ragu saboda da yawansu sun rasa ayyukansu sakamakon cutar.

    Ya kara da cewa kudin harajin da gwamnati ke samu ma ya ragu da kashi 40 cikin 100 saboda ba ta iya karbar harajin.

    Mista Beyle ya ce lallai wasu za su jigata sakamakon raguwar kudin da 'yan kasar ke aikawa gida.

    Kusan dala biliyan daya da rabi ne ake aikawa Somalia duk shekara, sama da agajin da kasashen waje ke ba ta, kuma iyalai da yawa sun dogara ne kan kudin domin harkokin rayuwarsu.

  11. Wasu 'yan China sun tsere daga cibiyar killacewa a Uganda

    Wata kotu a kasar Uganda ta samu wasu 'yan China shida da laifin tserewa daga wani otel da aka killace su sakamakon cutar korona, a cewar rahoton jaridar Daily Monitor.

    An kama su ne a watan da ya gabata tare da direbansu dan kasar ta Uganda da matarsa lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

    Ba su cika kwana 14 da aka shardanta ba na killace kai a otel din.

    Sun amsa laifin nasu ne a ranar Talata a gaban kotu na keta doka. Jaridar ta ce za a yanke musu hukunci a ranar 4 ga watan Mayu.

  12. Jamus za ta fara gwajin rigakafin cutar korona

    Rigakafin cutar korona da kamfanin kasar Jamus BioNTech tare da hadin guiwar kamfanin Amurka na Pfizer suka samar ya kai matsayar da za a fara gwajinsa ga mutane, kamar yadda hukumomin lafiya a Jamus suna bayyana.

    Za a fara gwajin maganin rigakafin ne kan mutane 200, 'yan tsakanin shekara 18 zuwa 55

    Ministan lafiya na Jamus Jens Spahn, ya ce wannan babbar alama ce da ke nuna ci gaban da aka samu na samar da ragakafi a Jamus, wanda za a fara gwajinsa.

    Ya kuma ce za a dauki watanni domin allura cewa da za a yi a jikin mutum don haka dole a kiyaye.

    Tuni dai masana a jami'ar Oxford a Birtaniya suka ce za su fara gwajin maganin rigakafi da suka samar a wannan makon. Sannan ana gudanar da gwajin rigakafin da aka samar a kasashen Amurka da China.

  13. Coronavirus: Sama da mutum dubu 12 suka kamu a Saudiyya

    Yawan wadanda suka kamu da cutar korona a Saudiyya yanzu sun haura mutum dubu 12, kamar yadda alkalumman ma'aikatar lafiya ta kasar suka nuna.

    Jimilar mutum 12,772 suka kamu da cutar a Saudiyya, yayin da 1,812 suka warke.

    Cutar korona ta kuma kashe mutum 114 a Saudiyya, inda cutar ta fi yaduwa a biranen Makkah da kuma Madinah.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Za a kai sojoji dubu 73 domin tabbatar da dokar kulle a Afirka ta Kudu

    Ramaphosa

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Afirka ta Kudu za ta yi amfani da karin dakaru 70,000 wajen tabbatar da mutane sun bi dokar hana zirga-zirga da manufar dakile yaduwar cutar korona.

    A shafinsa na Twitter, madugun 'yan tawaye, John Steenhusien ya wallafa wata wasika da shugaban kasar Cyril Ramphosa ya rubuta cewa ya yanke shawarar kai karin dakarun soji dubu 73 saboda samun karin masu dauke da cutar ta korona.

    Yanzu an haramta yin motsa jiki da yawo da kare da sayar da barasa. Sai dai jami'an tsaro na samun kalubale wajen aiwatar da dokar.

    Yanzu haka dai akwai mutum 3,465 da suke dauke da cutar korona.

  15. Gwamna Elrufa'i ya ce ya warke daga cutar korona

    Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Elrufa'i ya ce ya warke daga cutar korona.

    Malam Nasir Elrufa'i ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce "Ina farin cikin sanar da ku a yau cewa bayan kusan makonni hudu ina karbar magani, yanzu na warke daga cutar bayan yi min gwaje-gwaje guda biyu da suka nuna ba na dauke da cutar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. An samu mai cutar korona a Adamawa a karon farko

    Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da samun mutum na farko da ke dauke da cutar korona.

    Gwmanan jihar, Ahmadu Fintiri ya sanar da hakan ne a wani jawabi da ya yi ta kafar sada zumunta na Facebook, inda ya ce jihar za ta dauki tsauraran matakai wajen dakile bazuwar cutar annobar a jihar.

    Daga cikin matakan da gwamnan ya lissafa akwai rufe iyakokin jihar domin gudun kwararar makwabta zuwa cikin Adamawar, inda ya nemi hadin kan jami'an tsaro da su sanya ido.

  17. Coronavirus: Darajar dabbobi na karyewa a Nijar

    Makiyaya

    Asalin hoton, Getty Images

    A jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin makiyaya ne suka koka da halin da Fulani makikya ke ciki a dalilin cutar korona.

    Kungiyoyin na masu kokawa da yadda farashn dambobi ya rikito kasa a kasuwani.

    Yanzu dai bayanai na nuna kudin saniya guda da kyar kan sai bahu guda na na hatsi.

    Kungiyoyin sun kira ga gwamnati da ta tallafa musu ta hanyar kai musu abincin da take saidawa a farashi mai rahusa.

  18. Daurin shekara bakwai ga masu tsangwamar ma'aikatan lafiya a Indiya

    Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin kasar Indiya ta zartar da wata doka da ta tanadi daurin kusan shekara bakwai ga duk wanda aka samu da laifin kai wa ma'aikatan lafiya hari a kasar.

    Ma'aikatan jinya da likitoci sun bayar da rahoton cewa ana kai musu hari - wasu daga cikin hare-haren sun faru ne a yayin da ma'aikatan ke kokarin bin sahun wadanda suka yi mu'amala da masu dauke da cutar a cikin unguwanni, wasu kuma a asibiti ne abin ya faru.

    A wasu lokutan kuma makotan likitocin ne kan kai musu hari saboda tsoron kada su harba musu cutar.

    An ayyana dokar ne a ranar Laraba, wadda ke cikin wani bangare na tanadin dokar annoba a kasar da aka yi tun lokacin Turawan mulkin mallaka shekara 123 da ta gabata.

    Akwai kuma tarar kudi da za ta kai ta dala 6,000 (kusan naira miliyan 2.5).

    Ya zuwa yanzu Indiya na da mutum 15,474 da ke dauke da cutar korona da kuma 640 da suka mutu.

  19. Coronavirus: Za a kwashe milyoyin almajirai zuwa ga iyayensu

    Almajiri

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 sun sanar da rufe dukkanin makarantun tsangaya da manufar shawo kan cutar korona a yankin.

    Yayin wani taro da suka yi daga nesa ta kafar intanet a jiya Talata, gwamnonin 19 sun kuma amince da kwashe almajiran domin mayar da su ga iyayensu.

    Kididdiga dai ta nuna akwai almajirai milyan tara a yankin arewacin Najeriya, abin da ya sa ake fargabar yaran ka iya yada cutar ta korona.

    To sai dai jihar Jigawa ta ce ita ba za ta dauki almajirai ta mayar da su jihohinsu na asali har sai bayan annobar korona saboda ka da a kai inda babu cutar.

    Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta fara shirin mayar da almajiran fiye da 600 ga jihar Jigawar.

    Baya ga jihar Jigawa, gwamnatin ta jihar Kano ta mayar da almajirai 419 ga jihar Katsina.

    Za a iya cewa wannan ne karon farko da gwamnatocin jihohin arewacin Najeriya ke kokarin kwashe almajiran da ke jihohinsu zuwa jihohinsu na asali.

  20. Labarai da dumi-dumi, An dakatar da gwajin cutar korona a Kano

    Darektan cibiyar binciken cututtuka masu yaduwa da ke asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke jihar, Farfesa Isa Abubakar ya shaida wa BBC cewa sun dakatar da yi wa jama'a gwajin cutar ne sakamakon rashin kayan aiki.

    Farfesa Isa ya kara da cewa cibiyar za ta ci gaba da zama a kulle har zuwa lokacin da za a kai kayan gwaji daga Abuja.

    "Mun riga mun dauki samfirin wasu mutanen domin yin gwaji amma saboda babu kayan gwajin dole ne mu dakata har sai an kawo mana."