Coronavirus za ta jefa miliyoyin mutane a talauci - Bankin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Tasirin coronavirus ga hada-hadar kudi zai jefa kusan mutum miliyan 24 a talauci a kasashen gabashin Asiya da na Pacific, a cewar Bankin Duniya.
Bankin ya bayyana cewa ''za a samu matsin tattalin arziki a duka kasashen duniya''.
Bankin Duniyar ya yi gargadi kan jama'ar da suka dogara kan masana'antu da cewa suna cikin babban hatsari sakamakon tasirin da cutar za ta yi.
Cutar za ta yi tasiri ga yawan bude ido a Thailand da Tsibirin Pacific, da kuma wasu kamfanoni da ke a Vietnam da Cambodia.
Bankin ya bukaci yankunan da su kara inganta bangaren kiwon lafiya da kuma kayayyakin aiki, tare da bayar da tallafi ga marasa lafiya.
A wani hasashe da ya yi, bankin ya ce idan abubuwa ba su tabarbare sosai ba kusan mutum miliyan 24 za su tsallake fadawa talauci a yankin a 2020, sakamakon tasirin da annobar za ta yi ga tattalin arziki.


Idan kuma abubuwa sun tabarbare matuka kamar yadda bankin ya yi hasashe, bankin ya yi hasashen cewa kusan mutum miliyan 35 za su kasance cikin talauci, ciki har da mutum miliyan 25 a China.
Bankin ya yi bayani kan shiga talaucin inda ya ce idan mutum yana samun daga $5.50 zuwa kasa yana cikin talaucin.
Bankin duniyar ya yi hasashen cewa za a samu ci gaban tattalin arziki a Gabashin Asiya da Pacific da kuma raguwa da kashi 2.1 cikin 100.
Za a iya kwatanta wannan da karuwa a kashi 5.8 cikin 100 a 2019.
Bankin ya bayyana cewa da wuya a samu takamaiman hasashe kan ci gaban.
''Labari mai dadi shi ne cewa yankin na da karfin samun alkhairai, amma wasu kasashe dole su tashi tsaye su yi azama kwarai da gaske,'' in ji Victoria Kwakwa, mataimakiyar shugaba mai wakiltar yankin Gabashin Asiya da Pacific a Bankin Duniya.
Bayanai na baya-bayan nan dangane da tattalin arzikin China a ranar Talata ya nuna alamun ci gaba, sakamakon shawarar dawo da ayyukan masana'antu a watan Maris bayan kullewar da dama daga cikinsu a watan Fabrairu.

Karin labaran da za ku so ku karanta












