Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Taliban za su ci gaba da kai wa dakarun Afghanistan hari
Taliban ta ce dakarunta za su koma kai farmaki a kan dakarun tsaron Afghanistan, kwanaki biyu bayan da kungiyar ta sa hannu kan wata yarjejeniyar sulhu mai tarihi da Amurka a Qatar.
Wani kakakin kungiyar ya shaida wa BBC cewa tsagaita wutar da aka cimma da dakarun kasashen waje zai ci gaba da aiki, amma za su ci gaba da kai hari a kan dakarun Afghanistan har sai an sako fursunonin Taliban.
Shugaba Ashraf Ghani ya musanta cewa gwamnatinsa ta yi alkawarin musayar daruruwan fursunoni da kungiyar Taliban zuwa makon gobe, kamar yadda aka bayyana ranar Asabar a yarjejeniyar da aka cimma da Amurka.
Da aka tambaye shi ko yana jin cewa za a tattauna tsakanin gwamnatin Afghanistan da Taliban, Donald Trump ya ce abu mafi muhimmanci shi ne mayar da hankali kan ci gaban da aka samu wajen kwashe sojojin Amurka daga Afghanista din.
"Muna fita daga Afghanistan, muna so mu fice. Mun yi ganawa kyakkyawa da Taliban kuma mun za mu mayar da sojojinmu gida. Mun shafe kusan shekara 20 a nan.
"Lokaci ne mai tsawo, mun yi muhimmin aiki wajen kawar da 'yan ta'adda. Muna da tattaunawar da za mu ci gaba da yi, amma dai mun cimma nasarori da dama."
Da aka tambaye shi dangane da sanarwar da Taliban ta fitar, ministan harkokin wajen Pakistan Mahmood Qureshi ya shida wa BBC cewa bai ga sanarwar ba tukunna, amma yana da yakinin ana bukatar rage tashe-tashen hankula domin kai wa gaci.
Ya ce "ina kira ga duka bangarorin su kwantar da hankula kuma su nutsu su bude idanununsu sannan su tsaya kan manufa. Mece ce manufar? Manufar ita ce zaman lafiya da kwanciyar hankali."