Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afghanistan: Matar da ta jagoranci sulhu da mayakan Taliban
- Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Burin Fawzia Koofi na zama likita ya kau saboda kwace Afghanistan da mayakan Taliban suka yi a shekarun 1990.
Kungiyar ta Taliban wadda ta hana wa mata jin dadin rayuwa a kasar, ta kama maigidan Fawzia ta daure, sannan suka yi kokarin kashe ta inda daga bisani ta zama 'yar siyasa.
Fawzia daga bisani ta tattauna da 'yan Taliban, wadanda yanzu ke shirin kulla yarjejeniyar zaman lafiya da dakarun Amurka wadanda suka kawar da su daga mulki.
Fawzia ta ce "Babu tsoro ko kadan a zuciyata, a gani na yana da matukar muhimmanci ka zama jajirtacce, ni ina wakiltar matan Afghanistan ne".
Wasu 'yan Taliban na nemana ruwa a jallo
Fawzia Koofi na daya daga cikin mata kalilan da suka halarci wani taro da aka tattauna tare da tsoffin shugabannin kasar masu tsattsauran ra'ayi, inda aka tattauna a kan batun zaman lafiya a kasar.
A shekarar 2019 ne, Fawzia da wata mata mai fafutukar kare hakkin dan adam Laila Jafari, suka shiga wani otel a Moscow na kasar Rasha inda suka tarar da maza 70 sannan suka zauna a tattauna tare da su.
A bangare guda a wajen taron 'yan Taliban ne, daya bangaren kuma mata ne daga cikin 'yan siyasar Afghanistan da kuma masu fafutuka.
Fawzia ta ce "Na shaida musu cewa yanzu Afghanistan na da mutane iri-iri da suke kuma da akida daban-daban".
Ta ce "Wasu daga cikin 'yan Taliban na nemana ruwa a jallo".
A yayin doguwar tattaunawar, 'yan Taliban sun ki yarda su tattauna kai tsaye tare da gwamnatin Afghanistan, inda suka ce ba za su tattauna da gwamnatin "'yan amshin shata ba".
To amma bayan matsin lamba daga Amurka da Rasha, 'yan Taliban din sun amince sun tattauna tare da wasu wakilan gwamnatin Afghanistan din.
Ms Koofi tana daga cikin wadanda Taliban din ta tattauna da su daga bangaren gwamnati.
A matsayin ta na wadda 'yan Taliban suka taba wa rayuwa saboda kama mijinta, ta tare su gaba da gaba inda ta yi musu magana a kan sanya 'yancin mata a cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da ake tattaunawa.
Ta ce "Daga bangarenmu gwamnati akwai mata daga cikin wakilai, sai na shawarce su da su ma su kawo mace wajen tattaunawar, amma sai suka kwashe da dariya".
A lokacin mulkinsu daga 1996 zuwa 2001, Taliban ta haramtawa mata neman ilimi da aiki tare da sanya musu wasu dokoki.
Kasancewar ta 'yar kasar ta Afghanistan, Fawzia ta san irin mutanen da suka sha wuya a wannan lokacin.
Da lokacin mayar da bayaninsu ya yi a wajen taron, daya daga cikin masu shiga tsakanin daga bangaren 'yan Taliban sai ya ce mata wannan bukata ta Fawzia daidaito tsakanin jinsi ce.
Ta ce "Sai suka ce mace za ta iya zama Firai Minista, amma kuma ba zata iya zama shugabar kasa ba, sannan kuma mace ba za ta iya zama alkali ba".
Fawzia ta ci gaba da cewa "Ban amince da abin da suka ce, amma kuma ban musanta ba".
A tsarin 'yan Taliban a yanzu, mace za ta iya aiki sannan kuma ta yi karatu, amma kuma a bisa la'akari da tsarin abin da dokar Musulunci ta tanada.
'Ban taba sayen Burka ba'
Fawzia Koofi ta fara ganin mayakan Taliban ne a watan Satumbar 1996.
Fawzia ta ce "Ina karatun aikin likitanci a Kabul a lokacin da 'yan Taliban suka karbe ikon Kabul, na hango su daga gidana, an gwabza fada a kan tituna a lokacin".
A cikin kwanaki kalilan, aka shafe mata burinta tun tana karama, daga nan sai ta ci gaba da zama a Kabul tana koyar da yammata harshen Turanci.
Ta ce "Na shiga matukar damuwa a lokacin, idan har wani zai zo rana tsaka ya hana ka abin da ka ke buri, gaskiya akwai ciwo".
'Yan Taliban sun sanya wata doka da ta umarci mata su rinka sanya burka a cikin jama'a.
Daga nan ne, sai Fawzia ta takaita wa kanta zira-zirga domin ta tsira da ranta.
Wani bangare a kungiyar da ke kula da tarbiyar mutane a kungiyar ta Taliban, ya rinka bin tituna yana duba matan da ba su sanya burka ba yana dukan su.
Amma bayan da dakarun hadakar da Amurka ke jagoranta sun hambarar da gwamnatin 'yan Taliban bayan da suka kai harin 9 ga watan 11 a Amurka, sai mutane suka fara samun sauki.
Fawzia ta ce "A lokacin mun rinka fita tituna muna zuwa shaguna siyayya ba tare da fargabar duka daga wajen 'yan Taliban ba".
Bayan gwamnatin Taliban ta fadi, sai Ms Koofi ta koma aiki a Majalisar Dinkin Duniya inda suka rinka gyara halayyar tsoffin yara sojoji.
An kuma bar ta da 'ya'ya mata biyu wadanda ta kula da su har suka girma bayan mjinta ya mutu sakamakon tarin TB.
A lokacin da aka sanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar a 2005, sai Fawzia ta yanke shawarar shiga a dama da ita.
Mahaifinta dan majalisa ne, sai ta yanke shawarar ta goya masa baya ya samu kuri'un da ya ke bukata.
Ta ce "Babban kalubalen shi ne yadda zan fito da kaina na tsaya takara".
Daga na sai ta zama mataimakiyar shugaban majalisa, a lokacin ne ta tsallake rijiya da baya daga harin 'yan Taliban.
Ta ce "A watan Maris din 2010 ne na je Nangarhar domin gudanar da bikin Ranar Mata Ta Duniya, a kan hanyar dawowarmu ne aka kai wa jerin gwanon motocina hari".
An yi harbe-harbe sosai, amma kuma Fawzia da 'ya'yanta biyu sun tsira bayan da jami'an tsaron da ke tare da ita suka kare su ta hanyar dauke su da wajen suka kai su wata tashar karkashin kasa daga nan sai aka samo jirgi mai saukar ungulu aka saka su a ciki suka tafi.
Yanzu haka dai an kashe daruruwan fararen hula tare da jikkata wasu, sannan kuma kasar Afghanistan ta kasance daya daga cikin kasashen duniya marasa arziki.
Kazalika akwai 'yan kasar kusan miliyan biyu da dubu dari biyar da aka yi musu rijista a matsayin 'yan gudun hijra, yayin da wasu miliyan biyun kuma suka bar muhallansu.
An kuma kiyasta cewa akwai mata zawarawa da aka kashe wa mazaje miliyan biyu da suke ta fadi tashin tafiyar da rayuwarsu.