Kacici-Kacici kan Ranar Harshen Uwa ta duniya ta 2020

21 ga watan Fabrairun kowace shekara rana ce da aka kebe domin bikin harshen uwa a fadin duniya.

Kasar Bangladesh ce ta fara bijiro da maganar ranar harshen uwa ta duniya amma a 17 ga Nuwamban 1999 ne Hukumar Raya Ilmi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta fara sanar da ranar.

Daga bisani kuma Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a hukumance.

Albarkacin wannan rana muka shirya wannan kacici-kacicin don gwada kwazonku.