Za a raba maganin malaria kyauta a arewacin Najeriya

Malariya a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta bullo da wani sabon shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro, wato Maleriya a ilahirin jihohin arewacin kasar a wannan shekarar.

An yi wa shirin taken ''Yaki da Cutar Zazzabin Cizon Sauro a Lokutan Damina'' da nufin kare jama'a daga kamuwa da cutar, wadda cizon sauro ke haifarwa.

Cutar dai tana karuwa a lokutan damina, saboda gudanar ruwan sama, abin da ke jawo karuwar cushewar magudunan ruwa.

Dakta Mu'awiyya Aliyu, daraktan kula da lafiyar jama'a na jihar Katsina na daya daga cikin jami'an aiwatar da wannan shiri kuma ya ce za a bi gida-gida ne don bayar da magungunan zazzabin na maleriya.

"A daidai watannin damina za a tantance yara 'yan wata uku zuwa shekara biyar kuma jami'an lafiya za su ba su kwayoyin magani nan take su tabbatar sun sha sannan su ba iyayensu sauran kwayoyin don a ci gaba da ba yaran tsawon kwana biyu," in ji Dakta Mu'awiyya.

Ya ce wadannan kwayoyin maganin su ne za su bai wa yara kariya daga kamuwa da cutar.

Dakta Mu'awiyya ya ce wannan shirin kyauta ne kuma gwamnatocin jihohi sun amince za su dauki nauyin bayar da magungunan tare da tallafin wasu kungiyoyi da hukumomin lafiya.

Ya kuma ce za su tabbatar cewa sun wayar da kan mutane kan wannan shiri don gujewa irin halin da aka taba shiga a shekarun baya inda iyaye suka rika hana jami'an lafiya ba wa 'ya'yansu riga kafin cutar polio.

Ya ce "za mu shigar da al'umma mu yi musu bayani sosai musamman sarakuna da malamai da manyan mutane na cikin al'uma masu fada a ji."

Ya bayyana cewa a bana wannan shirin zai fara aiki a farkon damina.