Sudan za ta mika tsohon Shugaba Omar al-Bashir ga kotun ICC

Omar al-Bashir

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomin Sudan sun ce za su mika tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir ga kotun hukunta masu aikata manyan laifuka.

Tsohon shugaban kasar yana fuskantar zarge-zargen kisan kare-dangi, laifukan yaki da kuma na cin zarafin dan adam sakamakon yakin da ya barke a yankin Darfur a 2003.

An hambarar da shi daga kan mulki a watan Afrilun 2019.

Ya zama shugaban kasa ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a 1989 kuma an zarge shi da yin mulkin kama-karya.

Masu shigar da kara a ICC sun gabatar da bukatar cewa sai ya fuskanci shari'a kan kashe-kashen Darfur.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe kusan mutum 300,000 kuma mutum miliyan 2.5 yakin ya daidaita.

A watan Disambar 2019 ne aka yanke wa Bashir hukuncin daurin shekara biyu a cibiyar gyaran hali kan zargin cin hanci.

Masu shigar da kara a Sudan suna kuma tuhumarsa da kashe masu zanga-zanga a lokacin ake neman hambarar da shi.