'Yan mata da zawarawa 500 na son a aurar da su a Sokoto

Matan sun samu miji ta hanyar wani mai dalilin auren Sunnah
Bayanan hoto, Matan sun samu miji ta hanyar wani mai dalilin auren Sunnah

Zawarawa da 'yan mata da ke son aure sun ce gwamnatin jihar Sokoto ta manta da su, duk da cewa sun samu mazan da ke son su da aure.

Matan da ke bukatar auren sun ce shekara biyu ke nan da suka aika da bukatar neman taimakon gwamnatin jihar Sokoto ta aurar da su kuma har zuwa yanzu shiru ba labari duk da cewa an yi masu alkawalin auren.

Matan sun kunshi zawarawa da kuma 'yan mata da ba su taba yin aure ba, wadanda kuma suka ce sun samu miji ta hanyar wani mai dalilin hada auren sunnah.

Aliyu Bello kofar Rini, Shugaban wata kungiyar da ke hada auren sunnah a jihar Sokoto wanda zawarawan da 'yan matan suka ce sun samu miji ta hanyarsa ya shaida wa BBC cewa yanzu adadin mata kusan 500 ne ke bukatar tallafin auren duk da cewa da farko mata 100 ne suka nemi gwamnati ta aurar da su.

Amma gwamnatin jihar Sokoto ta ce tana sane da batun masu bukatar auren, inda kwamshinan kula da lamurran addini Hon Abdullahi mai Gwandu wanda zawarawan da 'yan matan suka tura bukatarsu ta hanyar ofishinsa ya ce akwai kwamiti da aka nada.

Ya ce suna gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar masu bukatar a aurar da su.

Matan sun samu miji ta hanyar wani mai dalilin auren Sunnah

Ana dai zargin wasu na fakewa da auren domin su sayar da tallafin kayan dakin da suka samu daga gwamnati.

A baya dai gwamnatin jihar Sokoto ta taba aurar da zawarawa sama 200, kuma a lokacin hukumomi sun ce sun bullo da shirin ne da nufin rage badala saboda rashin aure.

Amma kuma yanzu wasu na ganin hakan ya sa wasu sun koma dogaro da neman agajin gwamnati domin neman tallafn aure.