An bikin cikar Sarkin Zazzau Shehu Idris shekara 45 kan mulki

@

Asalin hoton, Twitter/GovKaduna

Bayanan hoto, Alhaji Shehu Idrsi (na biyu daga dama) tare da Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III (a damanasa da gwamna Nasir El-rufa'i (sanye da bakaken kaya)

Ranar Asabar ake bikin cikar sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, shekara arba'in da biyar a kan gadon sarauta.

Alhaji Shehu Idris shi ne sarki na 18 da ya dare kan mulkin Zazzau tun bayan jihadin Shehu Usman Danfodio.

An nada shi a kan mulki ne a 1975 bayan rasuwar sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu.

Wakilin BBC da ya ziyarci Zaria, Muhammad Kabir Muhammad, ya ce tun ranar Juma'a aka soma shagulgula inda aka yi addu'o'i a masallatai.

A cewarsa, ranar Asabar za a gudanar da taro wanda manyan shugabanni da sarakuna, ciki har da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufa'i, za su halarta.

Daga bisani za a gudanar da kasaitaccen bikin hawan dawaki, wato durbar.

Masarautar Zazzau dai na cikin manyan masarautun Najeriya kuma tana cikin abin da masana suka kira Hausa Bakwai.

Yarima Charles (Hagu) tare da Sarkin Zazzau, Shebu Idris, a fadarsa lokacin da Yariman na Birtaniya ya kai ziyarar kwana uku a watan Nuwamba na 2006.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarima Charles (Hagu) tare da Sarkin Zazzau, Shebu Idris, a fadarsa lokacin da Yariman na Birtaniya ya kai ziyarar kwana uku a watan Nuwamba na 2006.

Za ku iya karanta karin labarai: