Hukumar yaki da rashawa tana binciken ma'aikatan Masarautar Kano

Muhyi Magaji

Asalin hoton, Muhuyi Magaji Rimingado

Bayanan hoto, Muhyi Mgaji ya ce mutum biyu sun shiga hannunsu yanzu kuma suna neman wasu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta ce ta kama wasu ma'aikatan Masarautar Kano a Najeriya bisa zargin badakalar filaye mallakar masarautar.

Shugaban hukumar Muhyi Magaji ne ya tabbatar wa da BBC hakan, inda ya ce tuni suka kama mutum biyu kuma za su gurfanar da su a gaban kotu.

Hukumar na zarginsu ne da laifin karbar rashawa kan wani wani fili da suka sayar a unguwar Hotoron Arewa kan kudi naira miliyan 80.

BBC ta tuntubi Masarautar Kano don jin martaninta kan kamen ma'aikatanta, sai dai ta ce sai zuwa Talata ne za ta mayar da martani.

"Mun samu korafi cewa wasu mutane suna sayar da kadarorin masarauta kamar Gandun Sarki, saboda haka hukuma ta dauki matakin tuntubar duk masarautun Kano," a cewar Muhyi Magaji.

Wannan layi ne

Ya ce hukumar ta nemi ma'aikatan su bayyana gabanta domin yin bayani kan zargin da ake yi masu, amma a cewarsa lamarin ya ci tura.

Ya ci gaba da cewa lauyoyin masarautun ne suka hana bayar da bayanan da hukumar ta nema, abin da ya sa suka fadada bincike kuma suka gano an karbi na-goro a cinikin wani fili a Hotoron Arewa.

"Wadannan mutane sun karbi naira miliyan 13 kuma da ma mun gayyace su tun farko amma ba su zo ba, shi ne muka yi amfani da damar da doka ta ba mu muka tilasta masu su zo su yi bayani," in ji Muhyi.

"Yanzu dai muna tare da mutum biyu, kuma mun gama shirin kai su kotu. Su wadannan muna tuhumar su ne kan rawar da suka taka wurin sayar da filin amma wadanda suka sayar da filin za su zo su yi bayani."

Wannan layi ne

Ya kuma ce akwai kusan mutum biyar da suke kokarin kamawa bisa alaka da sayar da kayan da masarauta da gwamnatin Kano suka mallaka, sai dai bai bayyana sunansu ba.

Amma wata majiya a hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa ta shaida wa BBC cewa daga cikin wadanda ake shirin kamawa akwai Jarman Kano, Farfesa Isah Hashim.

Wasu na ganin wannan bincike ci gaba ne kan wanda gwamnatin Kano ke yi wa masarauta na zargin badakalar kudi wanda kotu ta dakatar, abin da Muhyi ya musanta da cewa "wannan lamarin daban ne".

An dade ana takun saka tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, abin da ya jawo raba masauatar ta Kano gida hudu kari a kan ta asali.

Yanzu haka akwai shari'a tsakanin masu zaben sarkin Kano da kuma fadar gwamnati a gaban kotu.

An ruwaito kungiyoyi da kuma daidaikun mutane da dama a Arewacin Najeriya da suke yunkurin sasanta bangarorin.