Zazzabin Lassa ya kashe mutum biyu a Kano - Hukumomi

Lassa Fever

Asalin hoton, Getty Images

Cutar Lassa ta kashe mutum biyu a asibitin koyarwa na Malam Aminu da ke birnin Kano a arewa maso yammacin Najeriya, a cewar hukumomi.

Gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan lafiyar jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Lassa.

Ibrahim Tsanyawa ya tabbatar da hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya yi a birnin Kano ranar Laraba da safe.

A cewar kwamishinan, a kalla akwai mutum 292 da ake tsammani sun kamu da wannan cuta kuma ana kula da su kamar dai yadda ka'idojin kula da cutar suka bukata.

Ya kara da cewa gwaji kan mutum biyun da ake zargi na dauke da cutar daga cikin uku, ya gano cewa sun kamu da cutar kuma sun mutu.

Yanzu haka dai akwai wasu karin mutum biyu da ke asibitin garin 'Yar Gaya da ke karamar hukumar Dawakin Kudu, inda suke karbar magani.

Kazalika, gwamnatin jihar ta Kano ta samar da kudade domin shawo kan cutar tare da wayar da kan al'umma dangane da alamomin cutar da matakan da ya kamata a dauka domin guje wa kamuwa da ita.

Gwamnatin ta kuma bayar da lambobin waya da za a kira da zarar an ga alamun cutar.

An dai fara samun rahoton bullar cutar ne a jihar ta Kano a ranar 21 ga watan Janairu, bayan da jami'in da ke kula da cututtuka a karamar hukumar Tarauni ya bayar da rahoton wasu mutum uku da ke dauke da cutar ta Lassa.

Tun a ranar Talata asibitin Malam Aminu Kano ya ce zai tsara taron wayar da kan ma'aikatan asibitin game da hanyoyin da za su bi don kariya daga annobar a ranar Laraba.

Sanarwar da asibitin ya aike wa ma'aikatansa ta kuma bukaci ma'aikatan asibitin su kwantar da hankalinsu da kuma yin taka-tsantsan yayin da suke duba sauran marasa lafiya.

Kazalika, su kuma kauce wa yada bayanai dangane da wannan batu a shafukansu na sada zumunta domin kauce wa tayar da hankalin jama'a.

A shekarar 2016 ma jihar Kano ta kasance cikin jihohin kasar da suka yi fama da cutar ta zazzabin Lassa kafin daga baya a shawo kanta.

A yanzu haka dai kimanin jihohon Najeriya bakwai ne ke fama da annobar ta zazzabin Lassa.

Masana lafiya sun bayyana cewa zazzabin Lassa ba shi da magani, saboda haka ne hukumomi suke wayar da kai kan hanyoyin da za a bi domin kariya daga kamuwa da cutar mai saurin kisa.

Akalla mutum uku ne suka mutu a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano sakamakon kamuwa da wata cuta da ake kyautata zaton zazzabin Lassa ce.

Cikin wadanda suka mutun har da jami'an lafiya biyu a asibitin.

A wata sanarwa da ta fitar ta cikin gida, hukumar asibitin na AKTH ta sanar da fara gudanar da bincike kan wasu mutane da ake zargin sun kamu da cutar zazzabin na Lassa.

Sai dai har kawo yanzu hukumomin lafiya a Kano ba su tabbatar da barkewar cutar ba a hukumance. Amma wasu bayanai na wasu manyan jami'ai da masu ruwa da tsaki a asibitin na Malam Kano sun tabbatar wa BBc barkewar annobar.

An fara zargin barkewar annobar ne bayan wata jam'iar jinya ta mutu sakamakon zazzabi mai zafi, sanna wani likita shi ma ya mutu 'yan kwanaki kadan. Sai kuma wani ma'aikacin lafiyar da yanzu haka ke kwance yana karbar magani.

Duka jami'an dai sun yi mu'amala ne da wata mara lafiya da taje asibitin daga jihar Bauchi. Bayanai sun ce matar na dauke da juna biyu lokacin da ta je asibitin, kuma an yi mata tiyatar gaggawa ta cire cikin da take dauke da shi domin ceto rayuwarsu.