China ta ce za a iya magance cuta mai toshe numfashi da ta bulla a kasar

'Yan China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutum biyu cutar ta kashe a China zuwa yanzu

China ta ce kwayar cutar nan mai toshe kafar nimfashi, wadda ta bulla a kasar kuma ta fara yaduwa zuwa kasashen waje, "za a iya yin maganin ta".

Hukumar Lafiya ta kasar ta yi gargadin cewa ana bukatar a kula da kyau ganin cewa ba a san tushen cutar ba da kuma yanayin yaduwarta.

Zuwa yanzu mutum biyu ne aka tabbatar cutar ta kashe, wadda ta bulla a yankin Wuhan a watan Disamba.

A wata sanarwa tun bayan bullar cutar, Hukumar Lafiyar ta yi alkawarin ci gaba da daukar matakan kare kai a lokacin sabuwar shekarar China ta Lunar.

Miliyoyin 'yan kasar ne ke ziyarce-ziyarce a lokacin bikin sabuwar shekarar - wadda ake kira Spring Festival - kuma za a fara bikin a mako mai kamawa.

Mutum 60 ne aka samu rahoton sun kamu da cutar, amma masu binncike a Birtaniya sun ce yawan mutanen zai iya kaiwa 1,700.

Kasar Singapore da kuma yankin Hong Kong suna tantance fasinjoji da suka taso daga Wuhan, su ma hukumomi a Amurka sun sanar da daukar irin wannan mataki a filayen jiragen sama na San Francisco da Los Angeles da kuma New York.