Lafiya Zinariya: Alamomi daukewar jinin haila

Bayanan sautiShirin Lafiya Zinariya a kan daukewar jinin haila

Latsa hoton da ke sama don sauraron cikakken shirin, wanda Habiba Adamu ta gabatar ta kuma tattauna da Dakta Yalwa Usman:

Alamomin sun bambanta daga mace zuwa wata, inda wasu matan kan fuskanci manyan sauye-sauye masu tsanani, wasu kuwa lamarin ya kan zo musu da sauki kafin su daina jinin haila.

Wannan lamari na daukewar jinin al'adar a cewar likitoci, mataki ne da ya zama dole kowace mace ta bi ta kan wannan siradi kafin ta kai ga matakin manyanta.

Sai dai ga dukkanin alamu ba dukkanin mata ne ke da masaniya kan irirn wannan hali da ke tunkararsu a rayuwa ba, duk da cewa wadannan sauye-sauye da mace ke ji ko gani kan dauki tsawon shekaru a wasu lokuta.

Rashin fahimtar wadannan sauye-sauye kan sanya wasu matan su dauki lamarin a matsayin cuta, yayin da wasu har danganta yanayin suke yi da aljanu.