Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wata tawaga daga jihar Kano a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar a ranar Juma'a.
Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter.
Ya ce tawagar wadda ta hada da wakilai daga 'yan kasuwa da 'yan siyasa da kuma sarakunan gargajiya ta samu jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero.
Da yake jawabi bayan taron, Ganduje ya ce sun kai wa Buhari ziyarar ta 'nuna godiya' saboda irin yadda yake marawa jihar Kano baya ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da tsaro.
Bayanan hoto, Cikin wadanda suka je har da Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.
Daya daga cikin wadanda suka kai ziyarar dan majalisar wakilai Abdullahi Mahmud Gaya, ya ce sun kai ziyarar ne domin yi wa Buhari godiya, kan yadda al'amuran zabuka suka gudana a Kano.
"Da kuma irin ayyukan da shugaban ya kai jihar da nade-naden mukaman siyasa da ya yi wa Kanawa," in ji shi.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, Bakin sun kuma samu ganawa da shugaban a zauren taron majalisar zartarwa.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, Sarkin Bichi ne kadai sarkin da aka yi tafiyar da shi cikin sarakunan jihar guda biyar.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, A nan Sarkin Bichin ne yake gaisawa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar Abba Kyari.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, Daga cikin maziyartan har da fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu Rarara, wanda yake yawan wake Shugaba Buharin.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya jagoranci tawagar.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, Akwai Dan Adalan Gaya da Sanata Barau Jibrin da kuma mata da dama a tawagar.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, CIkin mutanen har da shugaban Hukumar Hisbah Malam Sani Ibn Sina da babban limamin Masallacin Sheikh Ahmad Tijjani da shugaban kabilar Igbo mazauna jihar Kano da Bature Abdul'aziz.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, Akwai kuma Alhaji Sabi'u Bako da Farfesa Ibrahim Umar da Musa Gwadabe da 'yan majalisun jiha da na tarayya.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, A nan kuma Shugaba Buharin ne da shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alhassan Ado Doguwa, wanda ya dinga tashe a shafukan sada zumuntar Najeriya a makon da ya gabata, saboda zuwa majalisa da ya yi da matansa hudu.