Hotunan ziyarar Kanawa zuwa wajen Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wata tawaga daga jihar Kano a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar a ranar Juma'a.

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter.

Ya ce tawagar wadda ta hada da wakilai daga 'yan kasuwa da 'yan siyasa da kuma sarakunan gargajiya ta samu jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero.

Da yake jawabi bayan taron, Ganduje ya ce sun kai wa Buhari ziyarar ta 'nuna godiya' saboda irin yadda yake marawa jihar Kano baya ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da tsaro.

Daya daga cikin wadanda suka kai ziyarar dan majalisar wakilai Abdullahi Mahmud Gaya, ya ce sun kai ziyarar ne domin yi wa Buhari godiya, kan yadda al'amuran zabuka suka gudana a Kano.

"Da kuma irin ayyukan da shugaban ya kai jihar da nade-naden mukaman siyasa da ya yi wa Kanawa," in ji shi.