'Yan majalisa sun gana da hafsoshin sojin Najeriya

Hafsoshin sojin Najeriya

Asalin hoton, @DefenceInfoNG

Bayanan hoto, A makon da ya gabata 'yan majalisar tarayyar Najeriya suka yi kira da a sauya hafsoshin tsaron kasar

An yi wata ganawa tsakanin 'yan Majalisar Wakilan Najeriya da shugabannin hukumomin tsaron kasar don tattauna matsalolin da suka shafi harkokin tsaro.

A makon da ya gabata ne 'yan majalisar suka bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya canja hafsoshin tsaron saboda gaza shawo kan matsalar bayan shafe tsawon shekaru suna shugabanci.

Su ma takwarorinsu na Majalisar Dattawa rubdugu suka yi wa gwamnatin Shugaba Buhari, inda suka yi kira da lallai a dauki matakan kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Daga bisani ne kuma suka gayyace su don tattauna al'amuran da kuma yadda za'a shawo kansu.

Honarabul Abdulrazak Namdas shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin sojin kasa, ya kuma bayyana wa BBC cewa sun fahimci wani sabon al'amari a yayin tattaunawar da suka yi.

''Mun gano cewa akwai matsala, dole matsalolin nan sai an gyara su. Mun ga cewa in ba an samar masu da kudi ba abin da saura,'' in ji Namdas

Ya ce akwai bukatar samar wa dakarun sojin kasa isashshen kudin gudanarwa da kuma makamai don tunkarar matsalar.

Ya ci gaba da cewa: ''Mu ma 'yan siyasa da bangaren zartarwa akwai abubuwan da ya kamata mu yi don samar da sauki dangane da al'amuran da ke faruwa.

"Rawar da za mu iya takawa ita ce samar wa matsan da ke shiga aiyukan ta'addancin nan aiyukan dogaro da kai ta yadda ba za su shiga duk wata harka irin wannan da ake tunkarar su da ita ba."

Yadda matsalar ke kara kamari

Matsalar tsaro na ci gaba da ta'azzara, kama daga yin garkuwa da mutane da kuma yi masu kisan ba gaira ba dalili a yankin arewacin kasar, musamman arewa maso yamma da suka shafi jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna.

Sai dai duk da haka, hukumomi na cewa suna samun nasarar yaki da matsalar a Najeriya.

A farkon makon nan ma wasu rahotanni daga Najeriyar sun bayyana cewa barayin shanu sun kashe kimanin mutum 13 tare da kora shanun da ba a san yawansu ba a wasu kauyukka da ke jihohin Kaduna da Neja da kuma Zamfara.

Shida daga cikin mutanen 'yan sintiri daga Birnin Gwari suka mutu a yayin taho-mu-gama da barayin, wasu kuma suka sami raunuka a cikinsu.