Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Buhari ya jajanta wa shugaban China Xi Jinping
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi wa Shugaban China Xi Jinping fatan alheri da kuma al'ummar kasar yayin da suke dawainiya da annobar cutar nimfashi ta coronavirus.
"Yunkurin China na yaki da cutar coronavirus abin a yaba ne," kamar yadda Garba Shehu, mai magana da ywaun gwamnatin Najeriya, ya rawaito Shugaba Buhari yana fada.
Cutar coronavirus dai ta tashi hankalin China tun bayan barkewarta, inda zuwa yanzu ta kashe sama da mutum 300 sannan sama da 14,000 suka kamu.
Birnin Wuhan da ke yankin Hubei ne cibiyar cutar, abin da ya janyo hukumomi suka kulle garin ba shiga ba fita, sannan kuma kasashe na kwashe jama'arsu daga kasar.
"China ta dade tana agaza wa kasashen Afirka musamman a baya-bayan nan. Saboda haka ya kamata China ta sani cewa Najeriya tana tare da ita a wannan lokaci maras dadi," in ji sanarwar.
Ta kara da cewa: "Ganin irin kokarin da ake yi, nan da wani lokaci za a kawo karshenta."
Shugaba Buhari ya gode wa 'yan Najeriya game da yadda suke tarbar 'yan kasar ta China da kuma jajircewar da ake nunawa domin hana cutar bulla Najeriya.
Sannan ya yi addu'ar Allah ya kara wa mutanen China juriya da kuma hakuri ga wadanda suka rasa 'yan uwansu sakamakon cutar.