Matakan da Najeriya ta dauka don hana shigowar Coronavirus

Najeriya ta dauki matakan hana shigowar kwayar cutar Coronavirus zuwa kasar.

Hakan na zuwa ne yayin da kasashe ke rufe iyakokinsu da China, inda aka fara samun bullar bakuwar cutar wadda ta kashe mutun 170, bayan wasu 7,818 da suka kamu.

Zuwa yanzu dai an samu bullar cutar a kasashe 18.

Hukumar hana yaduwar cutuka ta kasar NCDC ta ce ta dauki matakan da suka kamata domin tunkarar cutar da ka iya shigowa kasar.

NCDC ta ce ayyana annobar da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi a matsayin babbar annoba a duniya na nuna bukatar daukar matakan hadin gwiwa domin hana kara yaduwar cutar a tsakanin mutane da ma tsakanin kasashe.

Matakan da ake dauka

Sanarwar da NCDC ta fitar ta ce hukumar tare da kawayenta sun yi hadin gwiwa wurin daukar matakan kar-ta-kwana domin bayar da dauki a kan kari idan aka samu wata barazana.

Sauran sun hada da tsananta sa ido da saurin gano cutar da samar da bayanai tare da inganta dakunan gwaji domin su yi aiki yadda ya kamata.

Hukumomin lafiya a China, a cewar NCDC, na tantance matafiya kafin su baro yankin Wuhan, inda cutar ta samo asali, domin hana yaduwarta zuwa sassan duniya.

Amma ta ce matafiyan da suka bar Wuhan cikin koshin lafiya amma suka samu matsala a hanya kuma za su gabatar da kansu domin tantance hakikanin abin da ke damunsu.

Sanarwar ta ce hadakar hukumomin lafiya da ke aiki a Najeriya ta girke ma'aikatan lafiya a tashoshin shiga kasar domin yin gwajin cutar da tantance matafiyan da za su shigo kasar daga China.

Sun kuma bukaci matafiya daga Najeriya zuwa yankin Wuhan na kasar China da su guji mu'amala da marasa lafiya da dabbobi da zuwa mayanka.

Alamomin Coronavirus

Alamomin cutar Coronavirus a cewar hukumar hana yaduwar cutuka, sun hada da tari da zazzabi da kuma toshewar nimfashi.

Shin ana warkewa?

Bakuwar cutar ba ta fiye yin kisa ba. Kashi 2% daga cikin 100 na mutanen da suka kamu ne ta yi ajalinsu, a cewar NCDC.

Maganin cutar

Har yanzu babu wani sanannen maganin bakuwar cutar ta Coronavirus, kamar yadda hukumar ta sanar.

Amma ana iya maganin yawancin alamomin cutar. Saboda haka ana maganin cutar ne gwargwadon yanayin da wanda ya kamu da ita ya tsinci kansa.

Akwai kuma wasu taimako da kulawa da ake bai wa mai dauke da cutar, kuma suna yin tasiri.

Kariya daga Coronavirus

Hanyoyin kare kai daga kamuwa da cutar mai yaduwa sun hada da:

  • Wanke hannu da sabulu da isasshen ruwa akai-akai.
  • Rufe baki da hankici yayin tari ko atishawa.
  • Guji shan magani ba tare da umurnin likita ba.
  • Garzaya zuwa cibiyar lafiya mafi kusa idan aka ga alamomin cutar.
  • Ma'aikatan lafiya su kiyaye ka'idodin hana yaduwar cuta a lokacin duba marasa lafiya, sannan su yi amfani da shawarwarin da aka bayar a kan tafiye-tafiye.
  • Matafiyan da suka dawo daga China lafiya lau amma suka fara tari da zazzabi bayan kwana 14 su tuntubi hukumar a kan lambar waya 080097000010.