Yadda CIA ke amfani da ruwa wajen yi wa jama’a tambayoyi

Wani masanin ilimin lafiyar kwakwalwa a Amurka wanda ya taimaka wa hukumar leken asiri ta CIA kirkiro wasu dabarun yin amfani da fasaha wajen yin tambayoyi, ya gabatar da jawabi gaban wata kotun soji da ke Guantánamo Bay.

James Mitchell ya ce ya amince ya gabatar da bahasi ne kawai saboda iyalan mutanen da suka mutu a harin 9/11 suna kotun.

Dr Mitchell da takwaransa Bruce Jessen sun samar da dabarun masu cike da takaddama ciki har da amfani da ruwa.

Mutum biyar da ke tsare a Guantánamo na gab da fuskantar shari'a sakamakon hare-haren na 9/11.

Mutanen biyar sun hada da Khalid Sheikh Mohammed, wanda ake zargi da kitsa hare-haren da aka kai kan Washington da New York a shekarar 2001.

Mr Mohammed ya ce an sha azabtar da shi lokacin da yake tsare a gidan wakafi na Guantánamo Bay da ke Cuba.

Wasu takardun hukumar CIA sun tabbatar da yadda aka rika azabtar da shi ta hanyar danna kansa cikin ruwa har sau 183.

Sauran mutane hudun kuma - Walid bin Attash da Ramzi bin al-Shibh da Ammar al-Baluchi da Mustafa al-Hawsawi - suma sun sha tambayoyi a hannun CIA a wasu gidajen yari da ake kira "black sites" a Turance kafin a mika su hannun sojojin Amurka.

Kafin fara sauraron shari'ar a Guantánamo, lauyoyin wadanda ake zargi na neman su samu hujjojin da wadanda suke karewa suka yi wa hukumar tsaro ta Amurka FBI, kuma aka yi watsi da su saboda dabarun tambayoyin da CIA ta yi amfani da su a kan mutanen.

Tawagar 'yan uwan mutanen da harin 9/11 ya rutsa da su suna ganin yadda zaman kotun ke gudana duk da cewa an sa shinge kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito.

Dr Mitchell, wanda ya bayyana a matsayin shaida, ya fadawa daya daga cikin lauyoyin masu kare kai cewa ya amince ya ba da bahasi "ga 'yan uwa da wadanda harin ya rutsa da su. Ba ku ba".

"Kun sha fadin abubuwa marasa tushe a kaina da Dr Jessen tsawon shekaru," in ji shi, a cewar Jaridar New York Times.

Sai dai wadanda ake zargi sun kalle shi ne ba tare sun nuna alamun kaduwa ba, a cewar 'yan jarida.

Ana sauraron za a ci gaba da sauraron shari'ar har tsawon mako biyu. Cikakkiyar shari'ar kuma an tsara gudanar da ita ne ranar 11 ga Janairun 2021.

Ana zargin dukkanin mutanen biyar da aikata laifukan yaki har da ta'addanci da kisan kusan mutum 3,000. Idan har aka same su da laifi, za su iya fuskantar hukuncin kisa.

Mece ce azabtarwa da ruwa?

Wata hanya ce ta yin tambayoyi da ke sa wanda ake yi wa tambayoyin ya dandana yadda ake ji idan aka nutse a ruwa.

Ana hada kan mutum da wani katako sannan a sa wani yanki a rufe bakin mutum. Ana zuba wa mutum ruwa a fuska, abin da ke sa mutum ya ji kamar huhunsa na cika da ruwa.

CIA ta fara amfani da ruwa wajen samun bayanai daga wanda ake zargi da laifi tun bayan hare-haren 9/11.

Wani kwamitin majalisar dattawa ya yanke cewa tsarin bai samar da bayanan sirri ba amma wasu jami'an CIA sun dage cewa tsarin ya bayar da bayanan da za su iya daukar mataki a kai.

Tsarin ya sabawa doka. Shugaba Barack Obama ya haramta azabtarwa ta hanyar amfani da ruwa don yin tambayoyi a 2009.

Shugaban Amurka Donld Trump kuma ya ce yana ganin yin amfani da tsarin zai yi tasiri saboda a cewarsa "dole a yi hukunci ga masu muggan laifi daidai da laifinsu".