Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
CIA za ta yi wa sanatocin Amurka bayani kan kisan Khashoggi
Kafofin yada labaran Amurka sun ce a yanzu shugabar CIA za ta yi wa majalisar dokokin kasar bayani kan kisan dan jaridar Saudiyya Jamal Khashoggi.
Sun ce Gina Haspel za ta yi wa sanatocin bayanin ne a ranar Talata.
Ta dai ki halartar wata ganawar da aka gudanar a makon da ya gabata tsakanin sakatarorin harkokin waje da na tsaron kasar a majalisar, abun da ya bata wa sanatocin rai.
An kashe Khashoggi ne a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Santanbul a watan oktoba.
Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa CIA ta gama gamsuwa cewa Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ne "mai yiwuwa ya bayar da umarnin" kisan.
Saudiyyar dai ta tuhumi mutum 11 amma ta yi watsi da zargin cewa yarinman na da hannu a kisan.
Kafofin yada labaran Amurka sun ce CIA tana da hujjar cewa ya yi musayar sakonni tsakanin sa da Saud al-Qahtani, wanda aka yi zargin ya ga lokacin da aka yi kisan.
Sakataren harkokin waje Mike Pompeo da kuma Sakataren tsaro James Mattis sun shaida wa sanatocin a makon da ya gabata cewa babu wata huja ta kai tsaye da ke nuna cewa da hannun yariman.
Shugaba Donald Trump ya ce binciken da CIA ta yi kan yariman bai kammala ba. A ranar 20 ga watan Nuwamba ya ce: "Zai iya kasancewa sosai yariman ya san komai a kan wannan mummunan lamari - watakila ya aikata, watakila kuma bai aikata ba.
Rahotanni sun kuma ce rab Gina Haspel ya baci kan yadda bayanan binciken CIA suka fita har kafofin yada labarai suka samu.
CIA ba ta yi tsokaci kan rahotannin abun da za a tattauna kan ganawar ta ranar Talata.
Wane ne Jamal Khashoggi?
Kwararren dan jaridar Saudiyya, Jamal Khashoggi ya shiga ofishin jakadancin kasarsa da ke birnin Santambul ran 2 ga watan Oktoba amma bai sake fitowa ba. Wane ne shi kuma me ya tursasa masa yin gudun hijira?
Jamal Khashoggi ya fara aikin jarida tun yana da kuruciya a matsayin mai aika rahotanni, a lokacin da ya kulla abota da Osama bin Laden na zamowar sa mai adawa da Saudiyya, abun da ya sanya shi barin kasar.
Kafin bacewarsa a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul, gudun hijirar da Khashoggi ya yi na nufin ya na raba lokacinsa tsakanin Amurka, da Burtaniya da Turkiyya.
Ya bar Saudiyya a watan Satumbar 2017, bayan da su ka samu tangarda da jami'an masarauta.
Daga kasashen waje, ya ci gaba da yada ra'ayoyinsa masu sukar gwamnatin Saudiyyar, a wata makala da ya rubuta a jaridar Washington Post ta Amurka, da kuma a shafinsa na Twitter inda ya ke da mabiya miliyan daya dubu dari shidda.