An yi jana'izar Jamal Khashoggi a Masallacin Ka'aba da wasu sassan duniya

Rahotanni daga Amurka sun ce Hukumar leken asiri ta CIA ta yi imanin cewa Yarima mai jiran Gado Mohammed bin Salman ne ya bayar da umurnin kisan dan jarida Jamal Khashoggi.

Wasu majiyoyi da kafofin yada labaran kasar suka ambato sun ce tuni hukumar ta sanar da bangarorin gwamnatin Amurka da suka hada Majalisa kan binciken da ta gudanar wanda ya ci karo da ikirarin gwamnatin Saudiya cewa ba hannun Yariman a kisan dan jaridar.

Iyalai da 'yan uwa da abokn arziki sun fara zaman makokin marigayi Jamal Khashoggi a gidansa da ke birnin Jedda.

Babban dan marigayin Salah Jamal Khashoggi ya koma kasar daga Amirka dan zaman makokin da za'a kwashe kwanaki 4 na yi.

A ranar Juma'a 16 ga watan Nuwamba ne daruruwan mutane suka taru don halartar jana'izar dan jaridar nan Jamal Khashoggi a masallacin Ka'aba da na Madina a kasar Saudi Arabia, da wasu biranen na duniya da suka hada da birnin Santambul da Lonodn da Paris da Washington.

An kashe shi ne a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyyan ba tare da an gano gawarsa ba, kuma har yanzu ba a gano gawarsa ba.

Shugaba Reccep Erdogan yana zargin gwamnatin Saudiyya da kisan, sai dai kasar ta musanta, amma hukumomin na Saudiya sun ce za su hukunta jam'ian tsaron kasar da suka kashe Jamal.

Daga bisani Turkiyyan ta ce an narkar da gawar ffitaccen dan jaridar.

Daya daga 'ya'yan mamacin Salah Khasoggi ya ce iyalensa sun fara karbar gaisuwar mahaifinsu, a gidan Jamal Khasoggi dake birnin Jidda ranar Juma'a.

Khashoggi, fitaccen mai sukar gidan sarautar Saudiyya ne, wanda aka kashe a karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Istanbul ranar biyu ga watan Oktoba.

Saudiyya ta amince cewa a ofishin nata aka kashe shi, ko da yake ta ce babu hannun 'yan gidan sarautar kasar.

Tun da fari mahukuntan kasar sun ce dan jaridar ya fita daga ofishin jakadancinsu bayan ya kammala abin da ya kai shi.

Kazalika masarautar Saudiyya ta musanta wasu kalamai da aka zargi Yarima mai jiran gadon sarautar kasar Mohammed bin Salman ya yi inda ya bayyana Khashoggi a matsayin musulmin da ke da matukar hatsari.

An ce ya yi kalaman ne a wata hira ta wayar tarho da ya yi da wani jami'in fadar White House gabanin Saudiyya ta amince cea an kashe Khashoggi.

Har yanzu dai babu wata matsaya daya da ke nuna takamaimai yadda Mr Khashoggi ya mutu. Ya je ofishin jakadancin ne domin karbar wasu takardu game da auren da zai yi.

Sai dai a ranar 10 ga watan Nuwamba Kasar Turkiyya ta bai wa Amurka da Burtaniya da Saudiyya da wasu kasashe bidiyon kisan dan jaridar nan mai sharhi Jamal Khashoggi.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya nanata ikirarin da ya yi cewa Saudiyya ta san wanda ya kashe Khashoggi.

Jamal Khashoggi ya fara aikin jarida tun yana da kuruciya a matsayin mai aika rahotanni, a lokacin da ya kulla abota da Osama bin Laden na zamowar sa mai adawa da Saudiyya, abun da ya sanya shi barin kasar.

Kafin bacewarsa a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul, gudun hijirar da Khashoggi ya yi na nufin ya na raba lokacinsa tsakanin Amurka, da Burtaniya da Turkiyya.

Ya bar Saudiyya a watan Satumbar 2017, bayan da su ka samu tangarda da jami'an masarauta.

Daga kasashen waje, ya ci gaba da yada ra'ayoyinsa masu sukar gwamnatin Saudiyyar, a wata makala da ya rubuta a jaridar Washington Post ta Amurka, da kuma a shafinsa na Twitter inda ya ke da mabiya miliyan daya dubu dari shidda.

Jamal Khashoggi, mai shekaru 59 ya fara aikin jarida ne a Saudiyya bayan da ya samu digirinsa a Amurka a shekarar 1985.

Lokacin da ya ke aiki da jaridar al-Madina a shekarun 1990, ya yi rubutu sosai a kan masu ikirarin jihadi a Afghanistan da suka shiga kasar don yakin Sobiyet.

Ya yi hirarraki da dama musamman ma da wani dan Saudiyya, Osama bin Laden, wanda ya ruwaito cewar ya san shi tun yana matashi a Saudiyya.

A lokacin, Bin Laden bai yi kaurin suna a kasashen yamma a matsayin shugaban al-Qaeda ba.