Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda budurwar Jamal Kashoggi ta ji da mutuwarsa
Ku latsa alamar hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Hatice Cengiz ita ce wadda Jamal Kashoggin yake shirin aura kafin a kashe shi, ta kuma raka shi zuwa karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Santanbul kafin ya shiga shi kadai.
Dan jaridar yana kokarin samun takardu da za su gasgata rabuwarsa da tsohuwar matarsa.
Ms Cengiz ta ce tana son duk wanda ke da hannu a kisan ya fuskanci shari'a.