Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Jamal Khashoggi? Dan jaridar Saudiyyan da ya yi batan dabo
Kwararren dan jaridar Saudiyya, Jamal Khashoggi ya shiga ofishin jakadancin kasarsa da ke birnin Santambul ran 2 ga watan Oktoba amma bai sake fitowa ba. Wane ne shi kuma me ya tursasa masa yin gudun hijira?
Jamal Khashoggi ya fara aikin jarida tun yana da kuruciya a matsayin mai aika rahotanni, a lokacin da ya kulla abota da Osama bin Laden na zamowar sa mai adawa da Saudiyya, abun da ya sanya shi barin kasar.
Kafin bacewarsa a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul, gudun hijirar da Khashoggi ya yi na nufin ya na raba lokacinsa tsakanin Amurka, da Burtaniya da Turkiyya.
Ya bar Saudiyya a watan Satumbar 2017, bayan da su ka samu tangarda da jami'an masarauta.
Daga kasashen waje, ya ci gaba da yada ra'ayoyinsa masu sukar gwamnatin Saudiyyar, a wata makala da ya rubuta a jaridar Washington Post ta Amurka, da kuma a shafinsa na Twitter inda ya ke da mabiya miliyan daya dubu dari shidda.
Tafiye-tafiye a Afghanistan
Jamal Khashoggi, mai shekaru 59 ya fara aikin jarida ne a Saudiyya bayan da ya samu digirinsa a Amurka a shekarar 1985.
Lokacin da ya ke aiki da jaridar al-Madina a shekarun 1990, ya yi rubutu sosai a kan masu ikirarin jihadi a Afghanistan da suka shiga kasar don yakin Sobiyet.
Ya yi hirarraki da dama musamman ma da wani dan Saudiyya, Osama bin Laden, wanda ya ruwaito cewar ya san shi tun yana matashi a Saudiyya.
A lokacin, Bin Laden bai yi kaurin suna a kasashen yamma a matsayin shugaban al-Qaeda ba.
Khashoggi ya ziyarce shi a kogunan tsaunukan Tora Bora, kuma ya yi hira da shi a Sudan a 1995.
Bayan wasu shekaru, jaridar kasar Jamus ta Der Spiegel ta yi hira da Khashoggi da kansa a 2011 kan alakarsa da Osama bin Laden.
Khashoggi ya amince cewar ya kasance mai ra'ayi daya da bin Laden a baya, na amfani da hanyoyin da su ka kaucewa dimokradiyya, kamar shisshigewa tsarin siyasa ko kuma amfani da hanyoyin tashin hankali don kwato wa yankin Larabawa 'yancinsu daga gwamnatocinsu masu cike da cin hanci da rashawa.
Kare sauye-sauye
Amma tun wancan lokacin, dan jaridar ya zama daya daga cikin masu tsage gaskiya a kasarsa, inda sau da yawa ya ke kafofin watsa labaran kasashen Yamma su ka kira shi a masani kan tsattsauran ra'ayi kan addinin musulunci.
Haka kuma, ana ganinsa a matsayin wanda ya san mutane sosai a Saudiyya, wanda ya ke shiga a dama da shi a masarautar Saudiyya.
Ya dade yana aiki da kafofin yada labaran yankin Larabawa, inda ya fara a matsayin wakili a kasar waje kafin ya kai matsayin edita.
Amma dole ta sa ya ajiye aikinsa a jaridar al-Watan sau biyu, a 2003 sai kuma daga baya a 2010, saboda wasu makaloli da ya rubuta wanda su ke sukar tsauraran manufofin 'yan Salafiyya, wanda ita ce darika mafi rinjaye a Saudiyya.
A shekarun da ke tsakani, Khashoggi ya bar kasar don yin aiki a matsayin mai bayar da shawara ga Yariman Saudiyya Turki al-Faisal, tsohon shugaban hukumar leken asiri wanda daga baya ya zama jakadan Saudiyya a Burtaniya da kuma Amurka.
A 2010, wani attajiri a Saudiyya Alwaleed bin Talal ya nada Jamal Khashoggi ya jagoranci sabon gidan Talabijin dinsa a Bahrain.
Guguwar Sauyi a kasashen Larabawa
Gidan talabijin na Al-Arab ta zamo kishiyar Al-Jazeera, wacce Qatar ke daukar nauyi.
Amma jin kadan bayan kaddamar da ita, aka rufe sabon gidan talabijin din karkashin jagorancin Khashoggi, bayan da ya watsa hira da wani dan adawa a Bahrain.
A wannan lokacin kuma, Khashoggi ya yi hira da manema labaran kasashen waje, inda ya soki tsarin sauarautar Saudiyya, kuma ya ce akwai bukatar tsarin dimokradiyya domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Lokacin da guguwar sauyi a kasashen Larabawa ta kada, Khashoggi ya goyi bayan 'yan adawar da ke neman a kawo sauyi a Masar da Tunisiya.
Ra'ayinsa ya sha bamban da na Saudiyya, wanda su ke ganin guguwar sauyin a matsayin barazana a gare su.
Bambancin ra'ayi a kan Trump
A Disambar 2016, lokacin da yarima mai jiran gadon Saudiyya ke kulla kawance da sabon shugaban Amurka Donbald Trump, rahotanni sun nuna cewa Khashoggi ya soki dangantakar.
Rahotanni a kafofin watsa labaran kasashen Larabawa sun nuna cewa an haramta rubuce-rubucen da ya yi kan batun.
Haka kuma, Jamal Khashoggi ya soki matakin gwamnatin saudiyya na warware alakarta da Qatar, inda ya nemi Saudiyyar da ta hada kai da Turkiyya kan batutuwan da su ka shafi yankin, kasar da ta ke da kawance mai karfi da Qatar.
Kwararren dan jaridar ya bar Amurka a watan Satumbar 2017, yana mai zargin yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman na Saudiyya yin tsattsauran hukunci kan 'yan adawa.
'Kamar Putin'
"Na bar gidana da iyalina da aikina, kuma ina kira da babbar murya," ya ce, "domin kin yin hakan zai zamo cin amanar wadanda su ke hakilo a jarun. Zan iya magana a lokacin da mutane da yawa ba za su iya ba."
"Zan ce Mohammed bin Salman na ayyukansa kamar shugaban Rasha Vladimir Putin. Ya na tursasa shari'a ga wanda ya ga dama," ya rubuta a makalarsa a jaridar Washington Post.
Ya ci gaba da sukar yariman har zuwa lokacin da ya shiga ofishin jakadancin a Santambul.
Wannan ne lokaci na karshe da wani ya gan shi.