Kamfanin Facebook ya kawo maslaha kan batun tantance fuska

Woman with biometric system on face

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamfanin Facebook ya fara amfani da na'urar gane fuska a Amurka a shekarar 2010 lokacin da suke alakanta mutane a hotuna suna amfani da na'urar

Kamfanin Facebook ya kawo maslaha kan rikicin da aka dade ana yi kan yadda yake gano hotunan mutane tare da ambatar sunansu a kan hoton.

Zai biya wata kungiya da ke jihar Illinois kudi dala milliyan 550, wadda ta yi musun cewa na'urar da take amfani da ita wajen gano mutane ta sabawa dokar sirri ta jihar.

An dade ana ta takaddama kan batun tun shekarar 2015, sai kuma aka sanar da sulhuntawar a yayin da aka fitar da bayanin samunsu na duk bayan wata hudu.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan sanda ke amfani da nau'rar wajen tantance fuskokin mutane da wuraren ayyuka na jama'a don gudanar da bincike sosai.

Karar da aka shigar kan cewa an bai wa Facebook dama a shekarar 2018 lokacin da wani babban alkalin tarayya ya yanke cewar za a iya sauraran karar a matsayin wadda mutane da yawa suka shigar.

Kotun daukaka kara ta ki yarda da kamfanin Facebook na kokarin dakatar da hakan, sai kuma a watan Janairu Kotun Koli ta ki bayar da damar sake duba daukaka karar.

Kungiyar masu sada zumuntar sun shaida wa BBC cewa: "sun yanke shawarar bibiyar kawo maslaha saboda abunda al'ummar ke nema kenan, sannan masu ruwa da tsakinmu a harkar, su wuce batun.

Kamfanin Facebook ya fara amfani da na'urar gane fuska a Amurka a shekarar 2010 lokacin da suke alakanta mutane a hotuna suna amfani da na'urar.

Na'urar na duba fuskar mai amfani da Facebook din sai ya ba da bayanai kan mutumin.

Fasahar ta nuna sarkakiya a lokacin. Duk da cewar masu amfani da ita na da damar rufewa, ba a tambayarsu ko suna son su yi amfani da na'urar.

A shekarar 2017 an sauyawa tsarin suna zuwa 'gane fuska' sai mutane suka samu damar budewa da rufewa cikin sauki.

Sai kuma 2019, kamfanin Facebook ta mayar da tsarin ya zama 'opt-in' wato ko za ka shiga cikin jerin sabbin abubuwan da suke so ya zama na sirri.

"Wannan sulhun na wakiltar gagarumin sulhu na biyu da aka yi da kamfanin Facebook a watanni shida.

"Kare bayanan sirrin mutane ya zame musu abu muhimmi kuma suna da injiniyoyi 1000 da ke aikin kan abun da ya shafi bayanan sirrin mutane," in ji Christopher Rossbach, na bankin zuba jari na J Stern & Co.